Connect with us

Uncategorized

Alkawarin Atiku ga Mutanen Jihar Kano

 

Dan takaran tseren kujerar shugaban kasar Najeriya na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kai ziyarar hidimar yakin neman zabe a Jihar Kano makon da ta gabata.

Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alkawarin ga al’ummar Kano da cewa zai sake mayar da jihar Kano ta zama cibiyar kasuwanci, masana’anta da aikin noma kamar yadda Jihar ta ke tun a baya.

Wannan itace bayanin sa a yayin da yake gabatarwa ga jama’a a hidimar yakin neman zabe da Jam’iyyar suka gudanar a filin wasan kwallon kafa na Sani Abacha da ke a Jihar Kano, a ranar Lahadi da ta wuce.

“Ku zabi Jam’iyyar PDP. Idan kuwa kun yi hakan, har na lashe zaben 2019, Na yi alkwarin mayar da daukakar Jihar Kano kamar yadda ta ke a da, wannan itace alkwari na to ribato duk sashen da ta lallace a Jihar” inji Atiku.

“Na kuma yi alkawarin samar da sauki ga wajen shirin tafiyar Hajj”

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa jama’ar Jihar Katsina sun fito makil ga hidimar ralin neman zabe da Atiku Abubakar da ya yi a Jihar makon da ta wuce.

Alhaji Atiku ya kuma dauki wannan zarafin zuwa Jihar don kai ziyara a fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II tare da mabiya baya kamar Sanata Bukola Saraki, Rabiu Kwankwaso, Gwamnan Jihar Kano na da, Ciyaman na Jam’iyyar PDP,  Uche Secondus da wadansu da ba a bada sunayen su ba, kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa da baya.

Advertisement
close button