Bayanin Atiku da Sarkin Kano, Sanusi Muhammad II (Lamido) game da zaben 2019 | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labaran Siyasa

Bayanin Atiku da Sarkin Kano, Sanusi Muhammad II (Lamido) game da zaben 2019

Published

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Lahadi da ta gabata, ya ziyarci Sarki Sanusi Muhammad II, Sarkin Kano a fadar sa.

Inda dan takaran ya bayyana da cewa “shugabannan gargajiya da Sarakuna na da gurbi mai muhinmanci ga cigaban wannan kasa” inji Atiku.

Wannan shi ne fadin Alhaji Atiku Abubakar a ziyarar sa a fadar sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a ranar Lahadi 10 ga watan Fabrairu, 2019.

“Na je ne in karbi albarku da addu’ar sarki” inji Atiku.

Dan takaran ya, Atiku ya kuma yi addu’a don zaman lafiyar kasa, da zamantakewar al’umma da ci gaban kasa a fadar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Shugaba Muhammadu Buhari, bayyana ga Jama’ar Jihar Benue da cewa idan har an kara jefa masa kuri’a, kuma ya lashe tseren takaran shugabancin kasar, ba zai canza ba daga adalcin sa.

Wannan shi ne fadin shugaba Muhammadu Buhari a ziyarar hidimar neman sake zabe da ya je a yankin Markudi, Jihar Benue.

A bayanin Sarki Sanusi, Sarkin Ya ce “Ku gujewa halin tashin hankali don tabbatar kyakyawar zabe a kasar nan ga Zaben 2019“.

”Zabe ba yaki bace, ba dole bane sai har an zubar da jini ko tada wata farmaki da sunan zaben” inji Sarki Sanusi.

”A matsayina na Sarki da kuma Uba ga jama’a, A kullum ina addu’a domin kwanciyar hankali da zamantakewa ta kwarai; dalili kuwa shi ne, babu wata cigaba a kasa idan har akwai tashin hankali” inji shi.

“Ku zabi wanda kuka gane da cewa zai samar da ci gaba da kuma jagorancin kwarai ga kasar Najeriya”  inji Sarki Sanusi.

“Ku je kuma ku karbi katunan zaben ku don samun damar jefa kuri’a, kuma ku yi ta addu’a don zaben nan ta kare cikin kwanciyar hankali”

Sarki, Sanusi Muhammad ya karshe da yabawa Atiku Abubakar da irin gudumuwar da yayi na samar da babban makarantar Jami’a a Jihar sa.

Muna da sani a Naija News da cewa ziyarar fadar sarkin Kano ya kasance ne da Peter Obi, abokin takaran Atiku, Shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki, Ciyaman na Jam’iyyar PDP, Uche Secondus da Sanata Rabiu Kwankwaso.

Haka kuma ziyarar ta halarci magoya kamar;  Ministan Harkokin Waje na da, Aminu Wali, Gwamnar Jihar Cross River na da, Liyel Imoke, Ministan Samar da Wutan Lantarki na da, Tanimu Turaki, tare da Sanata Abdul Ningi, ‎Hajiya Baraka Umar tare da dan takarar Gwmanar Jihar Kano na Jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.