Uncategorized
DSS sun kame Ben Bako, Mai yada labarai ga Jam’iyyar PDP ga lamarin zabe a Jihar Kaduna
Hukumar DSS, a ranar Asabar da ta gabata, sun kame kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP ga lamarin zaben Jiha, Ben Bako.
Hukumar sun kame Bako ne da zargin furci na tashin hankali da tada zama tsaye.
Muna da sani a Naija News da cewa shugabanci ta hana duk wani mutum da furci da zai iya jawo tashin hankali, ko ta kiyayya, musanman ga zaben tarayya na shekarar 2019.
An kame Ben Bako ne sakamakon wata bidiyo da ke dauke da wata furcin tashin hankali da ya yi akan zaben 2019 a wajen hidimar ralin yakin neman zabe da Jam’iyyar ta yi a garin Kafanchan, karamar hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna.
Bako, a cikin bidiyon ya umurci ‘yan Jam’iyyar da cewa su muzunta wa duk wanda bai yadda da Jam’iyyar su ba. Ma ana, su tada tanzoma kan duk wanda bai bada hadin kai ga Jam’iyyar PDP a lokacin zaben.
Mista Abraham Catoh, Kakakin Yada yawun Jam’iyayr PDP na Jihar, ya bada tabbacin kame Ben Bako, a bayanin sa da manema labaran THISDAY akan layi, a ranar Lahadi da ta gabata.
“Hukumar DSS sun ziyarci Ben ne da nemar bayani game da furcin sa da yayi a wajen hidiman ralin a ranar Asabar, bayan tattaunawar su kuma, sai suka tafi da shi zuwa birnin Abuja ranar Lahadi da ta wuce” inji Mista Catoh.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna ya fada da cewa “Duk kasar waje da ta kafa baki ga lamarin zaben Najeriya, za ta isa gida kamar gawa” Wannan itace bayanin El-Rufai da manema labaran NTA a makon da ta shige.