Connect with us

Uncategorized

Leah Sharibu ba ta Mutu ba – inji Gwamnatin Tarayya

 

A ranar Lahadi ta jiya, 10 ga Watan Fabrairun, Ministan yada Labaru da Al’adun kasa, Alhaji Lai Mohammed ya fada da cewa Leah Sharibu da ke kangin ‘yan ta’addan Boko Haram, bata mutu ba.

“Jita-jitan da ake yi game da mutuwar Leah Sharibu ba gaskiya bane, ba ta mutu ba” inji Lai Mohammed.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Leah Sharibu na daya ne daga cikin ‘yan Makarantan Dapchi, a Jihar Borno da ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace a kwanakin baya.

Ko da shike dai an saki dukan ‘yan matan da aka sace daga makarantar a lokacin, Leah ne kadai ‘yan ta’addan basu sake ba, wai don ta ki murabus da addininta na ‘Kirista’.

Ganin irin dadewar da Leah Sharibu ta yi da ‘yan ta’addan, mutane na ta jita-jitan cewa ai ta rigaya ta mutu, wata kila an kashe ta tun da dadewa.

Amma a ranar Lahadi da ta gabata, Alhaji Lai Mohammed ya karyata wannan jita-jitan, Ya ce “Ba gaskiya ba ne fade faden da ya mamaye yanar gizo da cewa Leah ta mutu, ta saura da rai” inji shi.

Ya fadi wannan ne a babban birnin Jihar Kwara, Ilorin,  a ranar Lahadi da ta gabata ga manema labarai, a wata sanarwa.

“Yaduwar wannan jita-jitan, shiri ne na ‘yan adawa don raunana amincin shugabanci, musanman Shugaba Muhammadu Buhari da ke a mulki da kuma karya gwuiwar su ga zaben da ke gaba” inji Mohammed.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Maman mataimakin shugaban kasa, Olubisi Osibanjo ta fada da cewa “Abin da Buhari da Osinbajo suka yi tsakanin shekaru 3, shugabannan kasar ta da basu iya yin hakan ba a shekaru 16 da suka wuce”.

“Shirin makirci ne da zargin karya daga ‘yan adawa don juya hidimar zaben kasar ga Zaben Musulunmai da Kiristoci, Ko kuma Arewa da Kudu” inji Lai Mohammed.

A karin bayanin shi, Ya ce Jam’iyyar APC na kyakyawar shiri game da ziyarar da shuga Muhammadu Buhari zai kai a garin Ilorin a ranar Litinin, watau ranar yau 11 ga Watan Fabrairun 2019.

“Jam’iyyar na ganawa don tabbatar da cewa ziyarar ya kasance da nasara” inji Shi.

Advertisement
close button