Connect with us

Uncategorized

Manomi ya kashe ‘yar shekara 4 a Jihar Katsina

Published

on

at

Hakilu Saidu, wani manomi mai shekaru 30 da ke zama a wata kauye mai suna Yankara, a karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina ya kashe wata diyar agolan makwabcin sa da ke da shekaru hudu 4.

Rahoto ya bayar da cewa Hakilu ya yi wa yarinyar duka ne har ga samun raunuka sosai. Abin takaici, yarinyar ta mutu a yayin da aka isar da ita a Asibitin Tarayya ta garin Funtua don kula mata da raunukan da ta samu sakamakon dukar.

Ganin hakan, Mallam Yahuza Yakubu, Mijin Maman Agolar da ta mutu, ya kai kara ga jami’an tsaron ‘yan sandan yankin Faskari to a kame Mallam Saidu, wanda ya aiwata mumunar halin.

“Ya kai ta ne a wata gini da ba a kamala ba, inda ya yi mata mugun duka har ga wannan faruwar” inji Mallam Yahuza.

A halin yanzu, Saidu na kulle wajen jami’an ‘yan sanda da karar aikata kisan kai.

Saidu na a kulle a halin yanzu a Gidan Jaru na Jihar Katsina har zuwa ga Watan ranar 4 ga watan Afrilu, 2019 kamin a dauki mataki ta karshe game da Hakilu Saidu da laifin da ya aikata.

Ko da shike har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa Hakilu ya aikata irin wannan halin ba.

Amma Insfektan Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar, Sani Ado ya bayyana ga Babban mai Shari’ar Kotun Kara a Jihar da cewa sun riga sun gama duk wata bincike akan Hakilu.

Mun ruwaito a Naija News Hausa Wata Mata a Jihar Bauchi ta tsage cikin ta da Reza akan zafin na’uda.