Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 11 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 11 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Jam’iyyar PDP na zargin Jam’iyyar APC da shirin makirci ga zaben 2019

Jam’iyyar PDP ta bayyana da cewa Jam’iyyar APC na wata shirin makirci ga zaben 2019 da za a fara a wannan Asabar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Jam’iyyarPDP ta kalubalanci Shugaba Muhammadu Buhari da kawo ‘yan Siyasa da ‘yan ta’addan kasar Nijar wajen Hidimar Ralin sa a Jihar Kano.

2. Leah Sharibu ba ta Mutu ba – inji Gwamnatin Tarayya

A ranar Lahadi ta jiya, 10 ga Watan Fabrairun, Ministan yada Labaru da Al’adun kasa, Alhaji Lai Mohammed ya fada da cewa Leah Sharibu da ke kangin ‘yan ta’addan Boko Haram, bata mutu ba.

“Jita-jitan da ake yi game da mutuwar Leah Sharibu ba gaskiya bane, ba ta mutu ba” inji Lai Mohammed.

3. Jam’iyyar APC ta tada Murya game da harin da aka shirya wa Jam’iyyar

Jam’iyyar APC da Jihar Oyo sun tayar da kararraki game da wani harin da ‘yan adawa ke shirin yi ga Jam’iyyar su.

Jam’iyyar sun bayyana da cewa akwai wata shiri daga ‘yan adawa don kai hari ga wasu manya daga cikin Jam’iyyar APCP.

4. Mutane bakwai suka mutu a wata Fashewar Motan Fetur a Jihar Anambra

Akalla mutane bakwai suka rasa rayukan su, wasu kuma da dama sun sami raunuka sakamakon fashewar wata Mota da ke dauke da mai da ta biyo hanyar Amawbia kusa da Awka, babban birnin Jihar Anambra.

Mun sami tabbaci a Naija News da cewa mumunar hadarin ya faru ne misalin karfe 10 na dare, a ranar Asabar da ta gabata.

5. Ga shugaba Buhari ne kawai ni ke bada rahoto – Inji Shugaban CCT

Shugaban Kwamitin Shari’a (CCT), Danladi Umar, ya bayyana cewa shi ba jami’in shari’a ba ne, saboda haka ba shi da wata sanarwa ko amsa tambaya ga kowa sai dai ga Shugaba Muhammadu Buhari kawai.

Wannan shi ne bayanin Danladi a yayin da Hukumar NJC da ke shari’a akan Alkali Onnoghen suka bukace shi da amsa wasu tambayoyi.

6. Bayanin Atiku ga Sarkin Kano, Sanusi Lamido game da zaben shekarar 2019

Dan takarar Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana da cewa sarakunan gargajiya na da rawar gani wajen ginar da kasar.

Wannan itace bayanin tsohon Mataimakin Shugaban kasar a ziyaran shi ga Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a ranar Lahadi da ta gabata.

“Na kai ziyara ne don neman albarku da addu’o’in Sarki” inji Atiku.

7. Ana zargin dan takaran Gwamnar Jihar Kwara da samar da takardun WAEC na Karya

Ana zargi Abdulrahman Abdulrazaq, dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Kwara da samar da takardan shaidar WAEC da ba ta gaskiya ba.

Wani hanyar sadarwa ta yanar gizo ta sanar da cewa dan takaran ya gabatar da takardar shaidar zuwa ga hukumar zaben kasa (INEC) don zaben watan Maris na Gwamnoni da za yi a shekara ta 2019.

Ko da shike, Rafiu Ajakaye, ma’aikaci ga Abdulrazaq ya karyata wannan  zargin, da cewa ba gaskiya bane hakan.

8. Nnamdi Kanu ya kara wata gabatarwa daga kasar London game da zaben 2019

Shugaban ‘yan kungiyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya kara wata gabatar wa ta biyu a wannan shekara a ranar 9 ga watan Fabrairun, 2019, Watau Asabar da ta gabata.

Kamar yadda muke da tabbacin hakan a Naija News, Nnamdi Kannu ya bayyana dalilin da ya sa bai kamata dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya fito takara ba a kasar Najeriya.

“Atiku Abubakar dan kasar Kamaru ne” inji Kanu.

Samu cikkakun labaran Najeriya daga shafin Naija News Hausa