Connect with us

Labaran Najeriya

Sakon Ta’aziyya ga Iyalan mutane 8 da suka mutu wajen Rali a Jihar Taraba – Buhari

Published

on

at

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta’aziyya ga Iyalan Mutanen da suka mutu a wajen hidimar ralin neman sake zabe na shugaban kasa da Jam’iyyar APC ta gudanar a Jihar Taraba, ta Jagorancin Shugaba Buhari dan Manyan ‘yan Jam’iyyar duka.

Hidimar ralin da aka yi a Jalingo, Jihar Taraba a ranar Alhamis 7, ga Watan Fabrairun, 2019 da ta gabata.

Shugaba Muhamamadu Buhari ya aika wakilai zuwa Jalingo a jagorancin Boss Mustapha, Babban sakataren Gwamnatin Tarayya tare da wasu a ranar Lahadi da ta gabata don kai gaisuwa ga Iyalan wadanda suka rasa rayukar su a wajen hidimar ralin.

Wakilan sun ziyarci Asibitin Tarayya ta Jihar Jalingo tare da Sarkin Muri, Alhaji Abbas Tafida da Gwamna Darius Ishaku don gayar da wadanda suka samu raunuka.

Shugaba Buhari ya kwatanta mutuwar wadannan mutanen a matsayin sadaukarwa ga Siyasar kasar Najeriya.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya yi addu’a da cewa Allah ya jikan ran su duka, ya kuma bada kwanciyar hankali da kulawa da iyalin su duka” inji Boss Mustapha.

Alhaji Haruna Kawuwa, ya nuna godiyar sa ga shugaba Muhammadu Buhari da sakon gaisuwar sa da kuma kulawa da ya nuna masu a wannan lokaci. Matar Alhaji Haruna ma na daya daga cikin wadanda suka mutu a wajen hidimar.

Ga wakilan da shugaba Buhari ya aika a Jalingo; Ministan Birnin Tarayya, Mohammed Bello, Gwamnan Jihar Adamawa, Mohammed Bindow tare da Dokta Ali Pantami, Daraktan Ilimin Fasaha, da Femi Adesina, babban mai bada shawara ga shugaban kasa ta sashin labarai da Sanata Ali Ndume.

Ga sunayen wadanda suka mutu a wajen Hidimar, kamar yadda manema labarai suka sanar; Alhaji Gudali Buba, Ardo Barkere, Alhaji Musa Namuddi da Sukaina Hassan, Amina Yahya, Zainab Yahya, Safiya Haruna Kawuwa da Ummul Al-Hassan.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ransa da wadanda suka rasa rayukan su ga yakin neman zabe da Jam’iyyar APC ta yi a Jihar Borno ranar jiya 21 ga watan Janairu, 2019.

Karanta kuma: Leah Sharibu ba ta Mutu ba – inji Gwamnatin TarayyaAdvertisement
close button