Connect with us

Labaran Najeriya

Bamu amince da Buhari ba ga zaben 2019 – Inji ‘Yan Shi’a

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kungiyar Zamantakewa ta Musulumman Najeriya (IMN), da aka fi sani da suna ‘Yan Shi’a sun fada da cewa basu da goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Sheikh Ibraheem Zakzaky ne shugaban wannan Kungiyar, kuma a halin yanzu yana a dahe ga jami’an tsaron kasa tun shekaru Ukku da ta wuce.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa ‘Yan kungiyar Shi’a sun yi zanga-zanga da barazanar cewa suna a shirye ko da zasu mutu ne har sai sun kubutad da shugaban su, Sheikh Ibraheem Zakzaky daga kulle.

Muhammad Ibrahim Gamawa, daya daga cikin ‘yan kungiyar Shi’a (IMN) ya bayyana da cewa ba su da sanin wannan rukunin da ta gabatar da zabin Buhari ga a matsayin dan takaran su ga tseren takaran shugaban kasa na shekarar 2019.

“Gabatarwa da wasu rukunin Siyasa ta Matasa suka yi a sunan Kungiyar Shi’a da cewa IMN ta mara wa Buhari baya ga zaben 2019, ba gaskiya ba ce. Bamu san da wannan rukunin ba” Inji Shi.

“Ku tuna da cewa shugabancin Buhari ne ta aika rundunar sojoji don kashe ‘yan kungiyar shi’a kwanakin baya har ma da kame shugabanmu da matarsa, kuma aka jefa su kulle har tsawon shekaru hudu. Duk da cewa Kotun Tarayya ta bukaci a sake shugaban namu tun a baya, amma shugabancin Buhari ta yi watsi da wannan”

“Ganin irin wadannan mugan hali da rashin kula, sake zaben irin wannan shugabanci, zabi ne na tashin hankali da ci gaban mugunta a kasa” inji Gamawa.

“Ba zamu makance da zaben irin wannan shugaba ba, wanda ya kashe mana ‘yan uwa kuma ya kame shugaban mu da tsawon shekaru ukku da ‘yan watannai”

“Zamu yi amfani da Kuri’un mu na kimanin Miliyan Takwas don zaben Dimokradiyya amma ba zaben ‘Yan Tada zama tsaye ba” inji Shi.

Karanta Wannan kuma: Wani Manomi ya kashe ‘yar shekara 4 a Jihar Katsina