Connect with us

Uncategorized

Farmaki ta barke a Ralin Jam’iyyar PDP a Jihar Legas

 

Wasu ‘yan tada zama tsaye sun tada fada a yayin da Jam’iyyar PDP ke hidimar ralin neman zabe

‘Yan ta’addan su tayar da fada ne tsakanin su kusa da inda Jam’iyyar ke hidimar ralin a nan Filin Tafawa Balewa da ke a birnin Legas.

An hango ‘yan tashin hankalin ne suna danbe da junansu, wasu ma da jifar junansu da kujeru. Rahoto ta bayar cewa wannan ya faru ne a misalin karfe 1:50 na ranar yau, a yayin da ake jiran dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da isowa wajen hidimar don gabatarwa.

Ko da shike ba a gane ko menene sanadiyar fadar ta su ba, amma an hango su ne suna fada da junansu, kusa da idan shugabanan Jam’iyyar PDP ke hidimar su.

Mai gudanar da hidimar ya ce “Na ga alama da cewa wasu sun zo wurinnan ne don tayar da hankali. Za mu kuma dauke su a matsayin ‘yan ta’adda”.

Ko da shike a bayyana da cewa an binciki jikin kowa kamin shigan wajen hidimar don magance irin hakan.

Amma an gano wasu kuma da ke shaye-shaye taba da kwayoyi, har ma da wasu masu sayar da kayan maye a wajen.

Mun ruwaito a Naija News da cewa wasu ‘yan tashin hankali sun yi jifar duwatsu a wajen hidimar ralin shugaba Muhammadu Buhari da aka yi a ranar Jiya a Jihar Ogun, idan aka yi kokrain jifar Adam Oshiomole kamin dada jami’an tsaro suka tarbi jifan.

Ko da shike dai, jifar dutsen ya nufi shiyar da shugaba Muhammadu Buhari ke zaune da manyan shugabannan Jam’iyyar, amma dutsin bai same su ba.

Advertisement
close button