Connect with us

Labaran Najeriya

Kada ku kunyartar da ni, Gwamna Amosun ya roki mutanen sa a ralin shugaba Buhari a Jihar Ogun

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan tada zama tsaye a Jihar Ogun sun yi wa Jam’iyyar APC jifa da dutse a wajen ralin neman zabe da shugaba Muhammadu Buhari ya je a Jihar.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar Ogun jiya Litinin 11 ga Watan Fabrairun, bayan barin garin Ilorin, babban Birnin Jihar Kwara inda shugaba Buhari ya ziyarta don kaddamar da hidimar yakin neman sake zaben sa.

Mun samu rahoto a Naija News da cewa an yi wa Adams Oshiomhole tsuwa a wajen hidimar ralin, a yayin da yake kokarin gabatarwa.

An gudanar da  hidimar ne a fillin wasan kwallo na MKO Abiola a birnin Abeokuta, nan Jihar Ogun a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari don neman kuri’a ga zaben shugaban kasa ta tseren shekarar 2019.

Tanzomar ta fara ne a yayin da aka marabci Oshiomhole don gabatarwa. Daga fara magana sai ‘yan ta’adda da ke wurin suka fara masa tsuwa, daga nan suka fara kokarin jifar sa, kokarin yin hakan sai jifar dutsin ya nufi inda shugaba Muhammadu Buhari ya ke, amma dai Jami’an tsaro da ke a wajen ba su bari dutsin ya fada ga jikin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.

Hidimar ke nan da ba a samu an kadamar ba kamar yadda ake bukata.

Wannan abin ya yi zafi da gaske har ma babban shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, Asiwaju Bola Tinubu ya fusata.

Gwamna Jihar Ogun, Ibikunle Amosun, shima bai ji dadin hakan ba, da ya ga haka sai ya dauki Makirifon don magana da mutane sa.

Kalli bidiyon ka ga yadda abin ya faru;