Connect with us

Uncategorized

Ku fito ku kori Jam’iyyar APC – Inji Jennifer Abubakar, Matan Atiku

 

Matan Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Dokta Jennifer Douglas Abubakar, ta bukaci Jama’ar Jihar Rivers da su fito su jefa kuri’ar su don kayar da Jam’iyyar APC ga zaben shugaban kasa da za a yi ranar 16 ga Watan Fabrairu, 2019, Watau wannan Asabar.

“Ku fito don ku tsige wannan shugabancin da ta kasa ga iya shugabanci” inji Jennifer.

Wannan shi ne fadin Jennifer a yayin da take gabatarwa a ranar Litinin da ta gabata a birnin Port-Harcourt, wajen hidimar neman zabe ga Jam’iyyar PDP ga zaben tarayya ta ranar Asabar mai zuwa.

“Jama’ar Jihar Rivers, ina mai jinjina maku da kuma godiya da irin goyon baya da kuke bawa Gwamnan ku. Ina kuma da tabbaci da cewa dukanku zaku jefa’a kuri’un ku ne ga Jam’iyya PDP a zaben 2019″ inji Jennifer.

“Ba sai ma mun roke ku ba don samun kuri’ar ku, Ina da tabbacin cewa kashi 100 na Jama’ar Rivers ‘yan Jam’iyyar PDP ne. Ku fito ku jefa kuri’un ranar zabe, Da matanku, Mazajen ku, harma da diyan ku duka. Kada ku yadda a dauke maku hakin zabin ku”.

Duk da cewa Alhaji Abubakar Atiku ya riga ya gabatar da alkawalan sa ga al’ummar Jihar da kasar Najeriya.

“PDP ba za ta yi alkawalan karya ba, ko da shike Jam’iyyar APC sun yi hakan a shekara ta 2015 da suka hau mulki. Ta mu shugabancin ba za ta kasance da haka ba” inji Atiku.

Muna ruwaito a Naija News Hausa da cewa Shugaba Muhammadu Buhari, a ziyarar hidimar neman sake zabe da ya je a yankin Markudi, Jihar Benue ya bayyana ga Jama’ar Jihar da cewa idan har an kara jefa masa kuri’a, kuma ya lashe tseren takaran shugabancin kasar, ba zai canza ba daga adalcin sa ba.

Ciyaman na Jam’iyyar PDP, Dan Sarki, Uche Secondus a nashi bayanin ya ce,  “Mun riga mun lashe Jihar Kano, kashi dari na Jihar Kano a halin yanzu ‘yan PDP ne”.

“Daman Kano na daya daga cikin Birane da Buhari ke ji da ita wajen jefa kuri’a, PDP ta lashe wannan Jihar a karon nan”

Kalli bidiyon yadda shugaban Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya jefar da Tutar Jam’iyyar APC a Jihar Ogun

Advertisement
close button