Mahaifin Rabilu Musa (Dan Ibro) ya Rasu

Allah ya jikan rai!

Alhaji Musa, Mahaifin Rabilu Musa da aka fi sani da suna ‘Dan Ibro’, ya rasu a ranar Lahadi 10 ga Watan Fabrairu da ta gabata, a misalin karfe 2:30 na rana.

Alhaji Musa ya rasu ne sanadiyar wata rashin lafiyar da ta kama shi da tsawon kwanaki. Allah ya Jikan sa, ya kuma yi masa rahama.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da tunawa da rayuwar Rabilu Musa ‘Dan Ibro’, Sai ga shi a yau kuma muna samu labarin rasuwar tsohon sa.

Allah kadai ya san ranar karshen kowa, addu’ar mu itace kowa ya kare lafiya.

Mu sami tabbacin mutuwar Alhaji Musa ne daga yanar gizon nishadarwa ta twitter da ‘yan Kannywood ke amfani da ita.

Ga sanarwar a kasa;

Wasu daga cikin masoyan Rabilu Musa ‘Dan Ibro’ sun yi juyayi da wannan, kuma sun aika sakon ta’aziya ta su.