Connect with us

Uncategorized

Mahara da Bindiga sun sace Mallaman Makarantar Jami’a Biyu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu ‘Yan Hari da Bindiga da ba a sani ba sun sace mallaman babban makarantar Jami’a biyu (2) ta Bowen University da ke a garin Iwo, a Jihar Osun.

Mun samu rahoto ne a Naija News da cewa Mallaman na kan hanyar dawo wa ne daga Ilesha lokacin da ‘yan harin suka tare motar su a anan shiyar Idominasi, a karamar hukumar Obokun na Jihar Osun.

Rahoto ta bayyana da cewa Mallamai hudu ne ke a cikin motar. ‘Yan ta’addar sun harbe daya da bindiga, guda kuma ya samu tsira, sa’anan suka samu sace sauran mallamai biyu da suka saura.

Mista Kolawole, wani ma’aikacin karamar hukumar Osogbo ya bayyana da cewa harin ya faru ne misalin karfe 4:30 na maraice. Ya fada da cewa shi ma sun tare motar sa, ko da shike dai ya samu tsira da baya.

“Yan hari da bindigan sun kai kusan su biyar, kuma suna yaren yarbanci ne, kuma suna sanye da bakar kaya sama da kasa. sun tsayad da motar da ke a gaban mu da mugayen makamai” inji Mista Kolawole.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa ‘Yan Hari da Bindiga sun kashe Yayar Kabiru Marafa, Sanatan da ke wakiltar Zamfara ta tsaka a makon da ta shige.

“A lokacin da suka tare motar da ke a gaban mu, Direban motar yayi kokarin gudu, daga nan suka harbi motar da bindiga. Ganin hakan sai muka fada daji da gudu. Muna jin su kuma da yaren yarbanci” inji shi.

“Har yanzun dai ba cikkaken labarin ‘yan hari, amma jami’an mu na cikin daji don nemar kamasu” inji fadin Folasade Odoro, Kakakin yada yawun jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar.