Connect with us

Uncategorized

2019: Matsayi na bai dace da zubar Jinin kowa ba – Inji Atiku

 

Dan takaran Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a gabatarwan sa lokacin da ake hidimar rattaba hannu ga takardan zaman lafiyar kasa ga zaben shekarar 2019 da za a soma ranar Asabar, ya ce “Matsayi na bai dace da zubar Jinin kowa ba a kasar nan”

“Ina mai ba da gaskiya da kuma fatar cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi amfani da matsayin sa na shugabanci don ganin cewa zaben 2019 zai kasance da gaskiya ba tare da makirci ba”

“Ina kuma begen cewa jami’an tsaron kasa da hukumar INEC za su gudanar da ayukan su da gaskiya, ba tare da bada hadin kai ba ga makirci ko nemar tashin hankali ba”

Akwai wata kalma da tsohon shugaban kasan Najeriya na da, Goodluck Jonathan ya fada a baya, a lokacin da tseren takara na shekara ta 2015. Wannan furcin ko ya zama abu mai muhinmanci a gareni.

Kalaman na kamar haka;

“Matsayina na dan takara da mai nema kujerar shugabanci, ban dace ba da zubar Jinin kowane mutum don lashe zabe” inji fadin Goodluck Jonathan a shekarun baya.

“Haka kuwa a yau, ina mai fadin cewa, ban dace da zubar jinin kowane mutumi ba a wannan tseren shugaban kasa ta shekarar 2019”

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Matan Atiku Abubakar, Dokta Jennifer Douglas Abubakar ta bukaci Jama’ar Jihar Rivers da su fito su jefa kuri’ar su don kayar da Jam’iyyar APC ga zaben shugaban kasa ta ranar Asabar, 16 ga Watan Fabrairu, 2019.

Ganawar Hidimar rattaba hanun ga takardar zaman lafiyar kasar da aka yi a yau 13 ga Watan Fabrairun, 2019, ya halarci manyan shugabannan kasar Najeriya, kamar su; Abdulsalami Abubakar, Manyan Sarakunan kasa, masu hangen nesa daga kasar Turai da sasshen Afirika da de sauran su.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa wannan ita ce karo na biyu da za’a rattaba hannu ga takardar yarjejeniyar zaman lafiyar kasa ga zaben shekarar 2019.

Advertisement
close button