Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Zamu kwato kudin da Obasanjo ya sace – Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya kalubalanci gwamnatin da, a jagorancin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo akan kudin samar da isashen wutan lantarki ga kasar Najeriya a baya da ake zargin Obasanjo da sace wa.

A ranar jiya, Talata, 12 ga Watan Fabrairu, ‘yan kwanaki kadan kamin a soma zaben 2019 a Najeriya. Shugaba Buhari yayi barazanar cewa zasu kwato kudi kimanin Dala Biliyan $16 da shugabancin tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo suka sace.

“In wutar ya ke? Ina kuma kudin mu yake? wannan itace kalmar shugaba Buhari a yayin da yake gabatarwa a hidimar ralin neman sake zabe da Jam’iyyar APC ta gudanar a birnin Yenagoa ta Jihar Bayelsa, da shugaba Buhari ya halarta.

“Gwamnatin mu zata bi likin duk wadanda suka sanya hannu ga wannan makirci da rashin gaskiya na sace kudin da ya kamata a samar da isashen wutar lantarki ga kasar. Zamu bi su, mu kuma ribato kudaden don ci gaba da aikin da suka ki yi” inji Buhari.

Muna da sani a Naija News da cewa Olusegun Obasanjo ya yi shugabancin farar hulla a kasar Najeriya daga shekara ta 1999 zuwa  shekara ta 2007, a karkashin Jam’iyayr PDP. Kamin marigayi, tsohon shugaban kasa, Shehu Musa Yar’Adua ya zo ya dauki gurbin Obasanjo.

Shugaba Muhammadu Buhari ya fada da cewa zasu bi wadanda suka sace kudaden kasar Najeriya, zasu kuma kwato kudaden don amfani da shi wajen samar da ayuka a kasa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kungiyar Zamantakewa ta Musulumman Najeriya (IMN), da aka fi sani da suna ‘Yan Shi’a sun fada da cewa basu goyi bayan shugaba Muhammadu Buhari ba ga zaben 2019.