Connect with us

Uncategorized

Dakta Zainab Shinkafi, Matan Gwamnan Jihar Kebbi ta bayar da Miliyan 2 don magance ciwon Kanser

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Matan Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta bayar da tallafi na kudi kimanin Naira Miliyan N2m ga mutane goma da ke dauke da ciwon Kanser a Jihar.

Mun sami tabbacin cewa Dakta Zainab ta bayar da wannan gudumuwa ne a ranar Talata da ta gabata ga mutane goma da ke dauke da ciwon Kanser a nan asibitin ‘Medicaid Cancer Foundation’ da ke a Birnin Kebbi a lokacin da take gabatarwa a wata hidimar karin fasaha ga yakin ciwon kanser a Jihar Kebbi, wadda Hukumar Kiwon Lafiya ta Jihar Kebbi ta shirya da hadin gwuiwar ‘Medicaid Cancer Foundation’.

A cikin bayanin ta, Dakta Zainab ta ce, yaki da ciwon kanser a Jihar Kebbi abu ne mai muhimanci ga gwamnatin Jihar da kuma masu kudi da jari a Jihar don ganin cewa a taimakawa wadanda ke kame da wannan ciwo da kuma ganin cewa an magance hakan.

“Asibitin Medicaid na aiki tare da hadin gwuiwar Dakta Ramatu Hassan da ke jagorancin da kuma wakilci a Gwamnatin Jihar Kebbi don kadamar da hanyoyi da za a iya yaki ta musanman da ciwon kanser a Jihar Kebbi” inji Zainab.

Ta cigaba da nuna godiyar ta ga Gwamnar Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu da irin taimako da tallafi ga yaki da ganin cewa an ci nasara akan wannan ciwon kanser.

Dakta Zainab ta bukaci wadanda suka halarci hidimar da cewa su mayar da hankali wajen samun fasaha ta musanman a wajen koyaswar da kuma  hada hannun da kananan hukumomin Jihar don yaki da cutar kanser.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da kimanin mutane da cutar Lassa Fever ya kashe a kasar Najeriya cikin wannan shekara ta 2019 da muke cikinta.