Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 12 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 13 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Hukumar EFCC tayi karar Babachir Lawal, a kotu Tarayya

Hukumar Yaki da Bincike akan Tattallin Arzikin Kasa (EFCC) ta kai Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, a gaban Kotun Babban Birnin Tarayya, Abuja akan wata zargi na makirci da kuma zamba da ya aikata.

Mun ruwaito a Naija News da cewa Hukumar EFCC ta kame Babachir Lawal ne a ranar Litinin da ta gabata.

2. Wuta ya ƙone kayan aikin zabe a ofishin INEC dake a jihar Anambra

Motocin Kwantena biyu da ke cike da kayan zaben kasa a yankin Awka, na Jihar Anambra sun kone da wuta.

Wannan lamarin ya faru ne a ranar Talata da ta gabata, a yayin da wuta ya kame ofishin hukumar INEC da ke kusa da Fillin Dokta Alex Ekwueme a nan  Awka, tare da ma’aikatan hukumar da suka guje daga ofisoshin su.

3. Shugaba Buhari ya yi barazanar binciken tsohon shugaban kasa, Obasanjo

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi alwashin cewa zai ribato kudi dala biliyan 16 da ake zargin gwamnatin da da sacewa a jagorancin tsohnon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo na Jam’iyyar PDP a shekarun baya.

Shugaba Buhari ya gabatar da wannan ne a yayin da yake jawabi a hidimar ralin Jam’iyyar APC a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa a yau.

“Za mu kame duk wadanda suka sace tattalin arzikin kasar Najeriya” inji Buhair.

4. Zamu dauki mataki ta musanman akan abin da ya faru a Jihar Ogun – Jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC sun yanke shawarar cewa zasu dauki mataki ta musanman akan wadanda ke da alhakin tallafawa tashin hankali da ya auku a hidimar ralin shugaban kasa da aka yi a Jihar Ogun a ranar Litinin.

Duk da haka, jam’iyyar sun ce, duk wata mataki akan hakan zai biyo baya ne a karshen zaben tarayya.

5. Kungiyar ASUP ta Umurci mambobin kungiyar da su dakatar da yajin aiki a makarantun su

Mallaman Makarantar kimiyya na kasa, a jagorancin Hukumar Mallaman Makarantan Jami’a sun dakatar da yajin aikin da suka soma watannai da suka gabata.

Ganin hakan, Hukumar ASUP ta umarci mambobinta da su koma ga Ofishin su da aiki a gaggauce.

6. Rikici ya barke a wajen hidimar ralin Jam’iyyar PDP a Jihar Legas

Wasu ‘yan ta’adda sun tayar da farmaki tsakanin junar su a wajen ralin shugaban kasa da Jam’iyyar PDP ta yi a a ranar Talata da ta gabata a Jihar Legas.

Ko da shike ba a bada tabbacin mafarin rikicin ba, amma dai abin ya faru ne misalin 1:150 na rana, inda aka hango ‘yan tada zama tsayen suna damne da junar su.

7. Osinbajo ya mayar da kanshi matsayin makiyin Yarbawa – inji Afenifere

Kungiyar Halaka da Zamantakewa ta Yarbawa, da aka fi sani da suna ‘Afenifere’, sun bayyana da cewa Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasan Najeriya, ya sanya kanshi a matsayin makiyin kasar yarbawa. Ganin irin yada Osinbajo ya mara wa yankin Hausawa da Fulani, da barin nashi ‘yan uwa.

Kungiyar sun gabatar da zabin su ga dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.

8. Mahaifin Rabilu Musa (Dan Ibro) ya Rasu

Alhaji Musa, Mahaifin Rabilu Musa da aka fi sani da suna ‘Dan Ibro’, ya rasu a ranar Lahadi 10 ga Watan Fabrairu da ta gabata, a misalin karfe 2:30 na rana.

Alhaji Musa ya rasu ne sanadiyar wata rashin lafiyar da ta kama shi da tsawon kwanaki. Allah ya Jikan sa, ya kuma yi masa rahama.

Ka sami cikakkun labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa