Connect with us

Uncategorized

Zaben 2019: Mahara da Bindiga sun sace Mista Monday, Ciyaman na APC ta Jihar Edo

Published

on

‘Yan hari da Bindiga sun sace shugaban kadamar da yakin neman zabe na Jam’iyyar APC ta Jihar Edo, Mista Deniss Idahosa da ke taimakawa Mista Dennis Idahosa, dan takaran Majalisa, a ranar Talata da ta gabata.

Mun samu rahoto ne a Naija News da cewa an sace Mista Monday Aigbobahi ne a ranar Talata a yankin Ofosu, karamar hukumar Ogbogui ta Jihar Edo.

“Wannan harin na da halaka da ‘yan adawa, saboda Monday na da karfi da farin jini sosai ga aikin siyasar karamar hukumar” inji Idahosa.

“Ba na shirye don ganin bulbular jini ga wannan zabe, bari kowa ya fito ya jefa kuri’ar sa cikin kwanciyar hankali”

Idahosa ya Umurci ‘yan ta’addan da su mayar da Monday ba tare da wata jinkiri ba. kuma ya bukaci magoya bayan sa na Ovia da dakatar da duk wata halin tashin hankali.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Mahara da Bindiga sun kame wani Dan Takaran Gidan Majalisa na APC a Jihar Edo, Michael Ohioa

Kwamishanan Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya, Mista Hakeem Odumosu ya bayyana da cewa bai samu cikkaken bayani ba tukunna akan harin, amma ya yi alkawalin cewa zai binciki DPO na yankin.