Connect with us

Labaran Najeriya

Biafra: Nnamdi Kanu zai yi gabatarwa a yau akan Jubril Aminu Al-Sudanni

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban Kungiyar Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu zai yi gabatarwa a yau game da Jubril Aminu Al-Sudanni.

Muna da sani a Naija News da cewa Kanu tun shekarar da ta wuce ya kafa baki ga hirar cewa an musanya wani da shugaba Muhammadu Buhari, da cewa Buhari ya rigaya ya mutu a London tun lokacin da yayi rashin lafiya na tsawon kwanaki a baya.

Bayan zargi da fade-faden Nnamdi Kanu game da shugaba Buhari, mun ruwaito a Naija News Hausa kuma da cewa Nnamdi Kanu na zargin dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da fadin cewa Atiku ba dan Najeriya ba ne.

“Atiku bai dace da fita tseren takaran shugaban kasar Najeriya ba don shi dan kasar Kamaru ne” inji Nnamdi. Kamar yadda muka Sanar a Naija News Hausa a kwanakin baya.

Nnamdi Kanu, yayi barazanar hallaka Jubril Al-Sudani da ya ke zargi da cewa shine aka musanya da shugaba Muhammadu Buhari da ya mutu tun kwanakin baya, a fadin shi.

“Zan Hallaka Jubril Aminu Al-Sudanni a ranar Alhamis ta gaba” inji Kanu a gabatarwan da yayi daga gidan radiyon Biafra a ranar Talata da ta gabata.

Ya kara barazanar hakan a ranar jiya a shafin nishadarwan sa na twitter;

Ga sakon kamar haka; 

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hadaddiyar Kungiyar Iyamirai da aka fi sani da ‘Ohanaeze Ndigbo’ sun bada umurni da cewa ba wata rukuni ko kasar waje da zata jefa kuri’a ga zaben kasar Najeriya da ta gabato.

Sun anbaci kasashe kamar; Kasar Nijar, Chad, Mali da Kamarun