Connect with us

Labaran Nishadi

PDP: Ku fito ku Zabi dan takaran ku – inji Atiku Abubakar

Published

on

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya shawarci al’ummar kasar Najeriya da fitowa ranar Asabar don zaben dan takaran su.

Muna da sani a Naija News Hausa kamar yadda muka sana a baya da cewa Atiku ya ce, “Matsayina bai da ce da zubar jinin kowa ba a Najeriya”.

Fadin Atiku ke nan a wajen hidimar rattaba hannu ga takardan zamantakewar lafiya ta biyu da aka gudanar a jiya, nan birnin Abuja don zaben 2019.

A yau Alhamis 14 ga watan Fabrairu, kwana daya kacal da fara zaben tarayyar kasar Najeriya, Atiku ya aika a shafin yanar gizon nishadin sa na twitter don gabatar da godiyan sa zuwa ga mambobi da magoya bayan Jam’iyyar PDP ga zaben 2019. Ya kuma bayyana godiyan sa ga tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, shugaban hukumar Zaman Lafiyar Kasar Najeriya da irin gwagwarmaya da yayi duka tare da mambobin kungiyar wajen tabbatar da cewa an gudanar da hidimar kuma an kare cikin kwanciyar hankali.

“Ina kuma shawartan ‘yan Najeriya duka da su fito don jefa kuri’ar su, su kuma zabi dan takaran da ya fi masu don kawo ci gaba ga kasar Najeriya” inji shi.

Ga sakon kamar haka a shafin twitter;