Connect with us

Uncategorized

Sabuwa: ‘Yan Ta’adda sun haska wuta ga Ofishin ‘Yan Sanda a Jihar Anambra

Published

on

at

Mun samu rahoto yanzun nan a Naija News Hausa da cewa wasu ‘yan tada zama tsaye sun haska wuta ga Ofishin Jami’an tsaron ‘yan sanda da ke karamar hukumar Ajali ta Jihar Anambra.

An bayyana da cewa sun kuma bude gidan jaru da ke a yankin don bada dama ga wadanda ke jaru don su gudu.

Ko da shike dai, A halin yanzu, Kakakin yada yawun Jami’an tsaron ‘yan sandan yankin, Mallam Haruna Mohammed ya bayyana da cewa “Ya na da tabbacin kamun wutar ne kawai, ko da akwai wata abu, labarin hakan zai biyo a baya” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Makiyaya sun kashe wani ASP na Jami’am ‘Yan Sanda a Jihar Delta

“Kwamishanan Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Jihar, Mustapha Dandaura na can wajen da abin ya faru. Kuma ana kan bincike akan wannan, duk wata labari zai biyo a baya” inji Mohammed.