Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sanda sun ci karo da Buhunan Takardun zabe 17 da aka riga aka dangwala yatsa

 

Jami’an tsaron ‘yan sanda sun ci karo da buhun 17 cike da takardun zabe da aka dangwala yatsu akai.

Muna da tabbacin wannan ne kamar yada wata likin tsaro ta sanar wa gidan jaridan DAILY NIGERIAN da cewa an rigaya an dangwala takardun duka ga Jam’iyyar APC.

A halin yanzu an kai buhun a Ofishin ‘yan sanda da ke a Jihar.

Kakakin yada yawun Jami’an tsaron ‘yan sandan yankin, Haruna Abdullahi ya bayyana da cewa takardun zaben ba ta kwarai bace, “foto kwafi ne na sheda don nuna wa mambobin Jam’iyyar da ke kauyuka yadda zasu dangwala wa APC” inji Abdullahi kamar yadda aka shaida wa Jami’an.

Ya ce “Bayan binciken mu, mun iya gane da cewa an shirya takardun zaben ne musanman don nuna wa mambobin Jam’iyyar da ke a Jihar Jigawa yadda zasu dangwala yatsa”

“Mutum biyu da ake zargin su ba daukar buhunan katin zaben sun bayyana da cewa an son ne a kai buhunan takardun zaben ne a yankin Dutse, ta Jihar Jigawa don bada haske ga mutanen kauyukan yadda zasu dangwala yatsar su ga zaben”

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da cewa yana da murna mara matukan gaske da irin shirye-shiryen da Hukumar gudanar da zaben kansa (INEC) ke yi don zaben 2019.

Advertisement
close button