Uncategorized
An dakatar da Alhaji Haruna, Mijin Matar da ta Mutu Wajen ralin APC a Jihar Taraba daga Aikin sa

Mun samu rahoto a Naija News Hausa da cewa Gwamnatin Jihar Taraba ta dakatar da Alhaji Haruna Kawuwa da Ofishin sa bayan mutuwar matan sa a ralin shugaban kasa na Jam’iyyar APC.
Mun ruwaito a baya da cewa mutane takwas 8 sun mutu a wajen ralin hidimar neman sake zaben shugaba Muhammadu Buhari a birnin Jalingo ta Jihar Taraba. Marigayiya Safiya, Matan Alhaji Haruna Kawuwa na daya daga cikin mutanen da suka mutu wajen ralin, kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa.
A yau mun samu rahoto da cewa Gwamnatin Jihar ta dakatar da Haruna daga matsayin sa a Ofis.
Mun samu sani da cewa Alhaji Haruna, ma’aikaci ne, kuma shugaba ne na al’amurorin karamar hukumar Ardo-Kola ta Jihar Taraba.
Ko da shike ba a bayyana dalilin dakatarwa daga aikin da aka wa Alhaji Haruna ba, amma dai ana jita-jitan cewa Gwamnan Jihar ya dakatar da Alhaji Haruna ne don ya baiwa matarsa dama na zuwa wajen hidimar ralin Jam’iyyar APC da aka yi don neman zabe ga shugaba Muhammadu Buhari.
An gabatar da wannan ne a wata wasika da Malam Lawal Yakubu, Sakataren karamar hukumar yankin ya rattaba hannu a ranar 13 ga Watan Fabrairu, 2019.
An sanya kanin kakakin yada yawun Gidan Majalisar Dattijai na Jihar Taraba, Mista Abel Peter Diah don daukar gurbin Malam Haruna.
“Dakatar da Alhaji Haruna ba abin da ya dace bane, kuma wannan ba halin siyasa bace” inji Mista Aaron Artimas a bayanin sa akan dakatar da Alhaji Haruna.
Jam’iyyar APC a Jihar sun bayyana rashin amincewar su da wannan matakin.