Connect with us

Uncategorized

Kimanin Mutane 100,000 sun janye daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyayr APC

 

Ana cikin ‘yan awowi kadan da fara zaben kasar Najeriya ta shekarar 2019, sai ga mambobin Jam’iyyar PDP na janyewa daga Jam’iyyar.

Mun samu rahoto a Naija News da cewa kimanin mambobi dubu dari (100,000) suka janye daga Jam’iyyar PDP da Jam’iyyar SDP, suka kuma komawa Jam’iyyar APC don marawa shugaba Muhammadu Buhari baya a Jihar Sokoto.

“An marabcin mambobin Jam’iyyar PDP da SDP da suka janye daga Jam’iyyar su zuwa APC a Jihar Sokoto ne ta hannun Sanata Aliyu Wamako” inji fadin Malam Bashir Mani, Mataimaki wajen yada labarai ga Jam’iyyar APC a Jihar Sokoto a ranar 13 ga Watan Fabrairu.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya shawarci al’ummar kasar Najeriya da fitowa ranar Asabar don zaben dan takaran su.

Mun sanar a jiya da cewa Jami’an tsaron ‘yan sanda sun ci karo da buhuna 17, cike da takardun zabe da aka dangwala yatsu akai.

An kuma bayyana da cewa buhunan da ke cike da takardun zaben na Jam’iyyar APC ne da su ke shirin kaiwa yankin Dutse, a Jihar Jigawa.

Ko da shike, shugaban ‘Yan sanda da ke jagorancin lamarin ya bayyana da cewa takardun zaben ba ta kwarai bace, foto kwafi ne da aka shirya don bada haske ga mutanen kauyen Dutse.

Karanta wannan: Ku guje wa Makirci wajen aikin Zabe, Kazaure ya fada wa ‘Yan Bautan Kasa (NYSC)

Advertisement
close button