Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 15 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 15 ga Watan Fabrairun, 2019
1. Ban umurci hukumar INEC ba ga dakatar da zaben Jihar Zamfara – AGF Malami
Abubakar Malami, lauya hukuncin kara na Tarayya, ya bayyana da cewa bai bada umurni ga hukumar INEC ba ga dakatar da zaben Jihar Zamfara.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Malami ya wallafa wata wasika na bukatar Hukumar INEC da dakatar da zaben Jihar Zamfara.
2. ‘Yan Hari da makamai sun sanya rigunan sojojin don harin motar hukumar INEC a Jihar Benue
Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta Jihar Benue sun gabatar da cewa wasu ‘yan hari da bindiga da ba a san da su ba sun sanya rigunan sojojin Najeriya don kai hari ga motar hukumar.
Kwamishinan hukumar INEC na Jihar, Nentawe Yilwatda ya bayyana hakan ne a cikin wata gabatarwa da yayi da manema labarai, kamar yadda Naija News ta halarta.
3. A karshe, Nnamdi Kanu ya bayyana ko waye ‘Jubril’
Shugaban kungiyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, a ranar jiya, Alhamis, 15 ga Watan Fabrairu ya gabatar a fili ko waye Jubril Aminu Al-Sudanni, wanda yake zargi da cewa an musanya shi da Shugaba Muhammadu Buhari.
Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa da cewa Nnamdi Kanu zai yi gabatarwa akan Jubril Kano a gidan radiyon Biafra a kasar London.
4. Tinubu ya mayar da martani akan jita-jitan cewa ya janye daga Jam’iyyar APC
Kakakin yada yawun Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, ya bayyana yadda wasu magoya bayan PDP a jagoranci tsohon kakakin maganar hukumar DSS, Marilyn Ogar suka hade da Tinubu a filin jirgin sama na Jihar Legas, inda suka haska wata hoto tare da tsohon Gwamnar Jihar Legas, Tinubu.
A cewar Mista Tunde Rahman, labarin hoton da Tinubu ya haska tare da shugabannin mata na Jam’iyyar PDP a filin jirgin ya bi ko ta ina a yanar gizon nishadi da cewa shugaba Bola Tinubu na son ne ya janye daga Jam’iyyar APC.
5. Ba ka da izinin bada umarni a dakatar da zaben Zamfara – Agbakoba ya fada wa Malami
Babban Jami’in Harkokin Nijeriya (SAN), Olisa Agbakoba ya gabatar da cewa hukumar zaben kasa (INEC) ta kasance hukuma ce da ke tsaka-tsaki, ba za ta karbi umarni daga gwamnatin tarayya ba.
Agbakoba ya fadi wannan ne don mayar da martani game da wasikar da Abubakar Malami ya wallafa zuwa ga hukumar INEC, na cewar ya kamata hukumar ta dakatar da zaben jihar Zamfara.
6. ‘Yan Sanda sun dakile hedkwatar hukumar INEC a jihar Rivers
Jami’an ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis da ta gabata sun katange ƙofar hedkwatar hukumar INEC da ke a birnin Port-Harcourt, ta Jihar Rivers.
Mun samu tabbaci a Naija News da cewa ‘yan sandan sun kuma rufe hanyar titin da ke shiyar Ofishin hukumar.
7. Shugaba Muhammadu Buhari yayi gabatarwa ga ‘yan Najeriya akan zaben ranar Asabar
Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar APC, shugaba Muhammadu Buhari yayi gabatarwa ga al’ummar Najeriya da cewa, “A yayin da kuke binbini ga dan takaran da zaku zaba, kuyi hakan da kyau da zurfin tunani ko Jam’iyyar adawa zasu iya samar da ci gaba fiye da yadda gwamnatin mu tayi” inji shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ya kuma kara da cewa kada Matasa su yadda wata rukunin siyasa ko dan takara ya yi amfani da su wajen kadamar da tayar da tanzoma ko halin ta’addanci ga zaben 2019.
8. Tsohon Alkalin kasa, CJN Onnoghen ya bukaci kotu ta dakatar da kamun sa
Walter Samuel Onnoghen, tsohon babban alkalin kotun kasa da aka dakatar a kwanakin baya, ya bukaci kotu ta dakatar da zancen kama shi don rashin bayyanar sa a gaban kotun, kamar yadda aka bukace shi.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kotun kara ta birnin tarayya ta bukaci Onnoghen da halarta a gaban kotun don yi masa gwaji.
9. Ni da Atiku zamu zama abokai bayan zaben ranar Asabar – inji Tinubu
Babban shugaban Jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, ya buga gaba da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai lashe zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 da za a yi a ranar Asabar.
Ya kara da cewa Atiku Abubakar zai koma gida da hutawa don ci gaban kasar Najeriya.
10. Gwamnar Jihar Taraba ya dakatar da Mijin Matar da ta Mutu Wajen ralin APC, Alhaji Haruna
Gwamnatin Jihar Taraba ta dakatar da Alhaji Haruna Kawuwa da Ofishin sa bayan mutuwar matan sa a ralin shugaban kasa na Jam’iyyar APC.
Ko da shike ba a bayyana dalilin dakatarwa daga aikin da aka wa Alhaji Haruna ba, amma dai ana jita-jitan cewa Gwamnan Jihar ya dakatar da Alhaji Haruna ne don ya baiwa matarsa dama na zuwa wajen hidimar ralin Jam’iyyar APC da aka yi don neman zabe ga shugaba Muhammadu Buhari.
Ka samu cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa