Connect with us

Uncategorized

Sanata Ahmed yayi Hadarin Mota

 

Sanatan da ke wakiltar Jihar Kogi ta tsaka daga Jam’iyyar PDP, Sanata Ahmed Ogembe yayi wata hadarin mota a yau

Mun samu rahoto a yau jumma’a da ranar nan da cewa Sanata Ahmed ya tsira daga wata hadarin mota a hanyar da ta bi Abuja zuwa Lokoja, a yayin da yake kan hanyar zuwa Okene don hidimar zaben.

“Hadarin ta faru ne da sanatan da safen nan, misalin karfe 9 na safiyar Jumma’a a yankin Gegu ta karamar hukumar Kotonkarfe a Jihar Kogi” a bayanin Duke Opeyemi, Mai bada shawara ga dan Majalisar Dokokin.

Opeyemi ya kara da cewa motar da sanatan ke ciki ya kihe a kasa har da juyawa sau da dama kamin ta tsaya. “Sanatan, tare da wadanda ke cikin motar basu ji wata rauni ba ko mutuwa” inji shi.

Sanata Ogembe ya nuna godiya mara matuka ga Allah da kare shi da wannan mugun hadari. Ya kuma yi addu’a da cewa Allah ya ci gaba da kare shi, Iyalan shi da kuma jama’ar yankin sa duka.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Jigin sama ya fadi da Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaba Muhammadu Buhari a makon da ta wuce a yayin da yake shiga Jihar Kogi don gudanar da hidimar yakin neman zabe.

 

Advertisement
close button