Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sandan Jihar Neja sun kame Masu sace-sacen mutane 4 a Jihar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Neja sun kame masu sace-sacen mutane guda hudu a Jihar.

An samu nasar wannan kamun ne bayan daya daga ciki mutanen da ‘yan sace-sacen suka kame da ya samu kubuta daga hannnun su.

Rahoto ta bayar da cewa sun sace wani mai suna baban Sani, da har suka karbi kudi naira Miliyan N1.5 kamin suka sake shi.

Daya daga cikin su, Mamuda Mohammed ya ce “Muna samun kudi da yawar gaske wajen sace-sacen mutane. Har ma muna ta kara mata a gida da kuma zaman isa da nishadarwa”. Wannan ita ce bayanin Mamuda ga manema labarai na garin Minna a yayin da ‘yan sanda ke shigar da su a Ofishin su.

“Mun samu kudi kwarai da gaske daga mutanen da muke kamawa. kuma duk wanda muka kama suna biyar kudi da har mukan kwatanta arzikin mu da irin ta Ministoci da da Daraktoci”.

Sunayen barayin itace haka; Mohammed Abubakar, Mamuda Mohammed, Mohammed Mohammed da Amadu Garba.

‘Yan sanda Jihar Neja sun kame wadannan mutane ne a kauyan Fota, nan karamar hukumar Lapai a Jihar Neja.

“Mun samu kame wadannan barayin ne bayan da muka samu kira daga Jami’an tsaron da ke yanki Lapai” inji Muhammad Abubakar.

“A gaskiya bamu taba zaton cewa zamu iya fada a hannun hukuma ba. Muna rayuwar mu yadda muka gadama kuma muna kashe kudi ga ‘yan matan mu da kuma kara aure duk lokacin da muka ga daman haka” inji barayin.

Shugaban Jami’an tsaron yankin, Muhammad Abubakar ya bayyana da cewa barayin sun furta da kuma tabbata da cewa lallai da gaske suna aikata wadannan halayen.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Jami’an Yan Sanda sun kame Masu Sace-Sacen Yara a Birnin AbujaDSP Anjuguri ya shawarci makarantu duka don zama da kulawa da kuma samar da tsaro a makarantu, musanman makarantun kananan yara don magance irin wannan.