Uncategorized
Zamu kai Atiku ga Ritaya bayan zaben ranar Asabar – Inji Tinubu

Shugaban Jam’iyyar APC, Sanata Bola Tinubu a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Legas ya gabatar da cewa Jam’iyyar APC zata kai dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ga ritaya bayan zaben ranar Asabar don ci gaban kasar Najeriya.
”Ni da Atiku, abokai ne kamin hidimar zaben nan, watakila zumuncin mu ya koma bayan mun kai shi ga ritaya ranar Asabar” inji shi.
”Kujeran shugaban kasa ba ta Muhammadu Buhari ko Atiku Abubakar ne kawai ba, tafi karfin mutun daya. Don ci gaban kasar Najeriya da kuma samu kwanciyar Atiku da kansa, zamu kai shi ga ritaya bayan zaben ranar Asabar”
Wannan itace bayanin Sanata Tinubu, da ya bayar a wata sanarwa daga bakin Ofisan yada labarai na shi, Mista Tunde Rahman.
”Watakila ma mu hada da abokin takaran sa, Peter Obi, saboda babu wata abin kwarai da Jam’iyyar PDP a jagorancin Atiku Abubakar da Peter Obi za su sama” inji Tinubu.
Ya kara da cewa, guri da manufan Jam’iyyar PDP ba daya ba ce da tamu. Mu na da kyakyawar shiri ne ga al’umma duka wajen samar da ayuka da ilimin fasaha ga matasa tare da tallafi iri-iri don karfafa tattalin arzin kasar mu Najeriya wajen samar da ayuka.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kalubalanci gwamnatin da, a jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo akan kudin samar da isashen wutan lantarki ga kasar Najeriya da Obasanjo ya sace tare da gwanatin sa.