Connect with us

Uncategorized

Hukumar INEC ta daga zaben Shugaban Kasa da Gidan Majalisai

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bayan shirye-shirye da gwagwarmaya akan zaben shekara ta 2019 da aka sanar da farawa a yau 16 ga Watan Fabrairu, Hukumar INEC da sassafen nan ta sanar da daga zaben zuwa gaba.

Haka kuwa hukumar ta daga zabuna da ke biye da zaben shugaban kasa da na Majalissai; watau zaben Gwamnoni, Gidan Majalisar Jihohi har zuwa 9 ga watan Maris.

“Bayan bincike da binbini na ganin cewa zaben shekara ta 2019 ya kasance zabe mafi daraja da kyakyanta, mun gane da cewa akwai bukatar mu daga zaben, saboda wasu ‘yan matsaloli da aka samu wajen samar da kayaki da shirye-shirye akan zaben” inji Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar INEC ta kasar Najeriya.

“Saboda haka, Hukumar ta daga zaben shugaban kasa da gidan majalisar dokoki zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019″.

“Wannan matakin zai bada karin dama ga hukumar don samar da kayaki yadda ya dace, kuma don kadamar da zabe mafi kyau a kasar” inji shi.

“Wannan mataki ya zama abu mai zafi da kuma mataki mai nauyi ga hukumar, amma ya zama dole da hakan don kadamar da zabe mafi dacewa ga kasa”

Farfesa Mahmood ya kara da cewa hukumar zata gana da Manya masu ruwa da tsaki misalin karfe 2 na ranar yau Asabar don tattaunawa akan wannan al’amarin.

Zamu sanar maku da duk wata labari da ta biyo baya daga nan Naija News Hausa

Kalli bidiyon Sanarwan daga bakin shugaban Hukumar INEC;

https://twitter.com/NaijaNews/status/1096623478915125248