Connect with us

Uncategorized

Boko Haram: Bam ya fashe a wata masallaci a Jihar Borno

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu ‘yan kunar bakin wake da ake zargin su da zama mamba ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai farmaki a wata Masallaci da ke a shiyar Jidari Polo, anan Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

An bayyana da cewa ‘yan ta’addan ukku ne, biyu daga cikin su na dauke da bam, guda kuma na rataye da muguwar bindiga.

“Sun fada wa masallacin ne a misalin karfe 5:40 na safiyar ranar Lahadi da ta gabata, lokacin sallar asuba’i” inji Kwamishanan jami’an tsaron ‘yan sandan yankin, Ofisa Damian Chukwu.

“Fashewar bam din ya tashi ne da ‘yan ta’addan guda ukku hade da mutane goma sha biyu da ke ciki da kewayan masallacin don sallar asuba’i”.

Ya kara da cewa wasu da cikin masu sallar da harsasu ya fada masu na a asibiti don samun cikakken kulawa ta gaggawa, a sakamakon raunuka daga harsasun bindiga.

Abba Aji Khali, shugaban hukumomin tsaro da ke Jihar, ya gabatar da cewa an samu harbe daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken kuma an ribato makamin aikin sa.

Mun sanar a Naija News Hausa ‘yan lokatai da suka wuce da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun yi wata ganawar wuta da ‘yan ta’addan Boko Haram a ranar Asabar da ta gabata a Jihar Yobe. Inda mutane 9 suka rasa rayukan su tare da Ofisan sojojin Najeriya.

“Duk da cewa mutane da yawa sun rasa rayukan su sakamakon wadannan harin, kuma mutane da dama sun samu raunuka. Wannan ba zai hana mutane fito wa don jefa kuri’ar su ba” inji Kwadinetan kungiyar ‘yan tsaro na Jihar.

Ka samu karin bayanai da labarun kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa