Connect with us

Uncategorized

HISBAH na shirin Aurar da Mata 8,000 a ranar guda, a Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kungiyar Islam da aka fi sani da suna, HISBAH ta gabatar da Zawarawan Mata, Gwamraye da ‘Yan Mata 8,000 da zasu yi daura wa aure a ranar daya.

Muna da sani a baya da cewa Gwmanatin Jihar Kano ta kadamar da shiri na aurar da mata 3,000 a ranar 12 ga watan Disamba, shekara ta 2018.
An gabatar da shirin aurar da mata kimanin 8,000 ne a ranar Asabar da ta gabata daga bakin Alhaji Adamu Yahaya a wata ganawa na tattaunawa da yayi da manema labaran (NAN) a Jihar Kano.

Alhaji Adamu ya ce, “Kimanin mata 15 muka samu da cutar inna (HIV), mun kuma sami 23 daga cikin su da ke dauke da junabiyu” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wani mutumi yayi wa matarsa saki biyu a gaban Iyayen ta, wai don bata gayar da kishiyar ta ba.

“Muna kadamar da gwajin lafiyar jikunan su ne don tabbatar da cewa suna da isashen lafiyar jiki kamin mu aurar da su” inji Adamu.

Ya kara da cewa, da zarar sun kamala bincike akan lafiyar jukunan su, gwamnatin Jihar zata gabatar da ranan da za a aurar da su duka.

A bayanin Alhaji Adamu, gwamnatin Jihar, a jagorancin Gwamnan Jihar, Abdullahi Ganduje, ta tsarafa wannan shiri ne don dakatar da halin karuwanci a Jihar.

An kuma gabatar da kwamiti na mutane 23, da kuma sanya jagoran su, Farfesa Sani Zaharaddeen, Babban Liman na Masallacin Jumm’a ta tsaka da ke a yankin don kadamar da shirin auren da kuma nemo mata daga kananan hukumomin Jihar da suka isa aure, ko kuma zawarawa da gwamraye da ke bukatan sake aure. Sai ayi masu bincike da gwajin lafiyar jiki, sa’anan a aurar da su duk a rana guda.