Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 18 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 18 ga Watan Fabrairun, 2019

1. Gidan Majalisar Dattijai sun daga zamar su, sun kuma sanya sabuwar rana don ganawa

Shugabancin Gidan Majalisar Dattijai sun daga ranar zaman su daga Talata, 19 ga Watan Fabrairun zuwa ranar Talata, 26 ga watan Fabrairu.

A fadin Mohammed Sani-Omolori, magatakardan gidan Majalisar, Ya bayyana da cewa majalisar ta daga ganawar ne sanadiyan zaben shugaban kasa da na gidan majalisa da aka daga.

2. Yadda Buhari, Jam’iyyar APC da Amina Zakari suka daga zaben 2019  – PDP

Jam’iyyar adawa, PDP sun zargi shugaba Muhammadu Buhari, jagorancin Jam’iyyar APC da Amina Zakari da kulle-kulle da ya kai hukumar INEC ga daga ranar zaben shugaban kasa da ya auku a ranar Asabar da ta gabata.

Inji fadin kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP, Mista Kola Ologbondiyan, a wata gabatarwa da yayi . Ya ce “Anyi amfani da Amina Zakari da wadansu don dakatar da zaben ranar Asabar.

3. An kashe kwamanda Ukku na kungiyar Boko Haram

Kwamandodi ukku na kungiyar Boko Haram sun mutu a wata ganawar wuta da rundunar sojojin Najeriya suka yi da ‘yan ta’addan.

Rundunar sojojin Najeriya sun yi ganawar wuta da ‘yan ta’addan Boko Haram ne a ranar Asabar da ta gabata a yankin Warawara ta Jihar Borno.

4. Okorocha, Amosun da Ajimobi ba zasu chi kujeran sanata ba – inji wani Annabi

wani Annabi mai suna, Temitope Aduroja, da yayi annabci da game da zaben shekarar 2015 akan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Ya kuma yi annabci akan daga zaben 2019. Ya ce “Gwamnoni da ke tseren kujerar sanata ba za su ci ba”.

Ya lisafta gwamnoni kamar, Isiaka Ajimobi na Jihar Oyo, Ibikunle Amosun, gwamnan Jihar Ogun; da Rochas Okorocha, gwamnan Jihar Imo.

5. Jam’iyyar PDP ta Jihar Ekiti sun yi kira da kulawa ga kayakin zabe da aka kai a Jihar

Jam’iyyar PDP sun yi wata hange game da kayakin zabe da hukumar INEC ta rabar a Jihar don zabe, kamin aka daga zaben ranar Asabar da ta gabata. kamar; samar da takardan rubuta sakamakon zabe da yawa, da kuma mayar da kayakin zabe a jinkiri kamin aka daga zaben ranar Asabar.

Jam’iyyar sun bayyana da cewa, a kularsu, kayakin zabe da aka mayar basu cika ba.

6. Sanata Dino Melaye ya samu tsira daga wata hari

Sanata da ke wakiltar Jihar Kogi ta Yamma daga Jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye ya tsira daga wata harin da wasu da ke sanye da rigunan sojoji suka yi masa a ranar Asabar da ta gabata.

Dino ya sanar da wannan ne a shafin yanar gizon nishadin sa ta twitter a ranar Asabar da cewa, “Wasu ‘yan hari da bindiga da ke sanye da rigunan sojoji sun hari motar da nike ciki da harbi a ranar Asabar”.

7. Hadaddiyar kungiyar Jam’iyoyi na zargin Buhari da musanya shugaban INEC

Bayan daga zaben shugaban kasa da ya auku ranar Asabar da ta wuce, hadaddiyar kungiyar jam’iyoyin siyasa sun bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari na shirin dakatar da shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu da musanya shi da Amina Zakari.

Mun samu tabbacin wannan ne a Naija News kamar yadda kungiyar CUPP ta gabatar da cewa ana shirin musanya Mahmood Yakubu da Amina Zakari a matsayin sabon shugaban kadamar da zaben kasa.

8. Sanata Adamu ya kalubalanci hukumar INEC akan daga zaben ranar Asabar

Sanatan da ke wakiltar Nasara ta yamma a Jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya ce “Dakatarwa da kuma daga ranar zaben shugaban kasa da hukumar INEC ta yi, abu mai kyau ne, amma hukumar ta yi hakan cikin kuraran lokaci”.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta daga zaben shugaban kasa da ya kamata a yi a ranar Asabar 16 ga watan Fabrairun da ta wuce.

Ka samu cikakkun labaran Najeriya a shafin Najia News Hausa

Advertisement
close button