Connect with us

Uncategorized

Mutun 9 suka mutu a sabuwar ganawar wuta da Rundunar sojoji suka yi da Boko Haram

Published

on

at

advertisement

Rundunar Sojojin Najeriya sun yi wata ganawar wuta da ‘yan ta’addan Boko Haram a ranar Asabar da ta gabata a Jihar Yobe.

Mun samu tabbacin cewa mutane 9 suka mutu sakamakon wannan munsayar wuta da ya faru tsakanin sojojin kasar da ‘yan ta’addan a ranar Asabar, 16 ga Watan Fabrairu, 2019, ranar da daman kasa ta sanya don soma zaben kasa ta shekarar 2019.

Rundunar sojojin sun kashe mutum biyar (5) daga cikin ‘yan ta’addan, Ofisa daya kuma da sojoji Ukku ne suka mutu a sakamakon harbin harsasu da ya auku tsakanin rukuni biyun a garin Buni Yadi da ke a karamar hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

“Ofisoshin rundunar sojojin Najeriya biyar (5) suka samu mugan raunuka sakamakon harsasau da ya fada masu, amma dai suna asibiti don kulawa ta musanman” inji Kakakin yada yawun sojojin, Col. Sagir Musa kamar yadda ya bayar ga Naija News.

“Rundunar sojojin ta samu ribato makamai kamar haka, bindigar AK 47 guda 9, Wata mugun bindiga gun, da mumunar wata kayar yak mai zubin layi 121 da dai sauran su” inji Col. Musa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun yi kashe wasu ‘yan ta’addan Boko Haram guda 4.