Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da makami sun kashe Boniface, Ciyaman na Jam’iyyar APC na Jihar Benue

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun samu rahoto a Naija News da cewa wasu ‘yan hari da bindiga sun kashe ciyaman na Jam’iyyar APC da ke a Jihar Benue, Mista Boniface Okloho, a karamar hukumar Ohimini a Jihar.

Dan takaran Gwamnar Jihar Benue a Jam’iyyar APC, Hon. Emmanuel Jime ya bayyana bakin cikin sa da wannan mumunar kisa da aka yi wa Mista Boniface.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘Yan Hari da Bindiga sun sace Ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar Abia, Hon. Donatus Nwankpa. Ko da shike da baya Mista Donatus ya samu kubuta daga hannun ‘yan harin.

Hon. Emmanuel ya yi kira ga gwamnatin jihar Benue da hukumomin tsaro da cewa su yi duk wata kokari da zasu iya yi don ganin cewa an kame wadanda suka aikata irin wannan mumunar halin.

“Na yi bakin ciki kwarai da gaske da irin wannan abin  da ya faru da dan uwar mu, mamba mu, Mista Okloho” inji shi.

“Mista Okloho na daya daga cikin manyan ‘yan Jam’iyyar mu da kuma daya daga cikin manyan ‘yan jam’iya a yankin mu ta Zone C. Mun rokon Allah ya sa ya huta lafiya, Amin” inji Hon. Jime.

Karanta wannan kuma: Zamu kai Atiku ga Ritaya bayan zaben ranar Asabar – Inji Tinubu