Connect with us

Labaran Najeriya

Zaben2019: Ba na jin tsoro, zan ci zaben 2019 – inji Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar APC ga tseren zaben 2019, shugaba Muhammadu Buhari, a yau Litinin 18 ga Watan Fabrairun, 2019, yayi zaman tattaunawa da manyan shugabannan Jam’iyyar APC a birnin Abuja. Inda suka kafa baki a akan lamarin zaben 2019, musanman ga matakin da hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta yi a ranar Asabar da ta gabata na daga zabe.

Taron ya halarci, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; jagoran hidimar zaben Jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, Shugaban Jam’iyyar, Bola Tinubu, da Gwamnonin Jiha da ke a Jam’iyyar da sauran ‘yan majalisa da mambobi duka.

“Dole ne mu binciki hukumar INEC bayan zabe, don sanin kwakwaran dalilin da ya sa ta daga ranar zaben kasa” inji shugaba Buhari.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa ana jita-jita na cewar shugaban na kokarin ya dakatar da Farfesa Mahmood Yakubu daga matsayin sa don sanya Amina Zakari.

Shugaban ya bayyana kamar yadda muka sanar a baya da cewa, dole ne sai gidan majalisar dokoki ta amince da hakan kamin a iya dakatar da shi. musanman akan dokar kasa.

Adams Oshiomole, yace “Da irin tsawon shekaru ukku da watannai da aka kafa baki ga shirin zaben 2019, bai dace ba ace hukumar INEC ta daga ranar zabe ba, musanman ‘yan awowi kadan da ya kamata an soma zaben” inji Adams.

“Zamu ci gaba da gudanar da yawon ralin mu har ranar zabe ta iso” inji Adams Oshiomole.

Ya kara da yabba wa shugaba Muhammadu Buhari da irin kokarin da yayi da gwagwarmaya na ziyarar jihohin kasa 36 gaba daya don yakin neman zabe.

Shugaba Muhammadu Buhari, a karin bayanin sa,  ya ce “Da irin goyon baya da mutane suka bani wajen hidimar ralin zabe da muka gudanar a jihohin kasar duka, ina da bugun gaba da tabbaci da cewa zani ci zaben 2019” inji shi.

“Bani mu da tsoro ko kadan, muna da tabbacin cin zaben shekarar 2019”.

Karanta wannan kuma: ‘Yan Sanda sun ci karo da Buhunan Takardun zabe 17 da aka riga aka dangwala yatsa