Uncategorized
DAPCHI: Ina ganin diyata a mafarki – inji Baban Leah Sharibu

Mista Nathaniel Sharibu, tsohon yarinyar da ke a kangin ‘yan Boko Haram ya fada da cewa yana ganin diyar shi a mafarki kusan kullum.
Mun tuna da cewa Leah Sharibu na daya daga cikin ‘yan makaranta da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kwashe daga Makarantar Sakandiri na Mata na garin Dapchi ta Jihar Yobe kwanakin baya.
Ko da shike dai da baya an sake sauran ‘yan makarantar, amma ‘yan ta’addan basu saki Leah Sharibu ba.
Kamar yadda aka bayyana, ‘yan ta’addan sun ki sake Leah ne wai don taki amincewa da janye wa daga addinin ta na Kirista zuwa addinin musulunci, kamar yadda suka bukace ta da yin haka.
“Yau ya kai shekara daya rabuwarmu da ganin diyar mu, amma kusan kowane dare ina ganin Leah a mafarki tana cewa, ‘Baba ya kuke?” inji Mista Sharibu, kamar yadda ya gayawa manema labarai.
Mista Sharibu ya bukaci ‘yan Najeriya, musanman manema labarai da cewa sun tuna wa gwamnatin tarayya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari game da alkawarin da aka yi mashi da cewa za a ribato yarinyar daga kangin ‘yan ta’addan boko haram.
Mun tuna a Naija News da cewa ‘yan ta’addan (ISWAP), rukunin Boko Haram ne suka sace Leah Sharibu hade da sauran ‘yan mata a ranar 19 ga watan Fabrairu, a shekara ta 2018.
Mun kuma tuna da cewa ‘yan ta’addan sun yi barazanar cewa Leah zata kasance kangin su har abada idan har gwamnati ba ta dauki matakin ribato Leah ba.
Mun ruwaito a baya da cewa gwamnatin tarayya sun yi barazanar cewa Leah Sharibu bata Mutu ba, kamar yadda Ministan yada Labaru da Al’adun kasa, Alhaji Lai Mohammed ya fada.
“Yau shekara daya cik amma bamu kara jin komai ba game da diyar mu, gwamnatin tarayya na alkwalri ne kawai amma har yanzu ba su cika ba” inji shi.
“A baya dai shugaba Muhammadu Buhari ya kira mata na, Rebecca Sharibu, a kan layi da bada tabbaci da cewa zasu ribato diyar mu, amma harwayau bamu gana da diyar mu ba” inji shi.
“Ina kira ga manema labarai da ‘yan Najeriya duka da su tunawa gwamnatin Najeriya game da diyar mu da ke tare da ‘yan ta’addan Boko Haram.
Karanta wannan kuma: Jami’an Yan Sanda sun kame Masu Sace-Sacen Yara a Birnin Abuja