Connect with us

Uncategorized

Hidimar samar da abinci ga ‘yan makaranta, barnan kudi ne kawai – Yahaya Ndako

 

Shugaban Kungiyar Ma’aikata (NLC) ta Jihar Neja, Kamrad Yahaya Ndako Idris yayi kira ga gwamnatin tarayya da cewa ta dakatar da hidimar samar da abinci gan ‘yan makarantan Firamare da sakandari da ake yi.

“Wannan shiri, barnan kudi ne kawai” inji Ndako Idris.

Kamrad Ndako Idris ya fadi hakan ne a yayin da yake gabatarwa a ranar Litinin da ta gabata a wata zaman ganawa da ta kungiyar mallaman makaranta (NUT) da aka gudanar a Jihar Neja.

“Hidimar hanya ce na cin hanci da kuma barnan kudi, gwamnati na iya bayar da kudin don samar da ayuka da kayakin koyaswa da zai amfani dukan ‘yan makaranta” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kungiyar Mallaman Makarantan Sakandiri (NUT) sun bukaci gwamnatin Najeriya da dakatar da shirin sanya ma’aikatan N-Power a makarantu, don sanya kwararrun Mallamai. kungiyar sun bayyana hakan ne ganin cewa yawancin mallaman N-Power da ake kaiwa basu da kwararran Fasaha ga koyaswa.

Inji bayyanin Kamrad Yahaya Idris, Gwamnatin tarayya na kashe kimanin naira Miliyan tara (N9m) a kowane wata don wannan hidimar. Da zai fi kyau ayi amfani da wannan kudin wajen gyara makarantu da suka lallace da kuma samar da kayakin karatu da makaratar a kowace Jiha.

”Hidimar ya jawo cin hanci da rashawa, a yau mun amince da cewa gwamnatin tarayya ta dakatar da wannan shirin saboda kowane iyali kan ba yaran su abinci kamin su zo makaranta” in ji shi.

Ya karshe da godewa kungiyar da shirya irin kyakyawar zama. “Yana da kyau mu mika komai ga Allah don shi kadai ne mai jagora da samar da komai a kasa”. inji Kamrad Yahaya Idris.

Karanta wannan kuma: ‘yan ta’addan Boko Haram sun tada Bam a wata masallaci a Jihar Borno

Advertisement
close button