Connect with us

Uncategorized

Hukumar INEC ta gabatar da ranar da za a dakatar da fitar ralin zabe

 

Bayan matakin da hukumar INEC ta dauka na daga ranar zaben shugaban kasa Asabar da ta gabata. hukumar ta kuma bada umurni da cewa kada wata rukuni, ko Jam’iya siyasa ta sake fitar yawon rali har a kai ga kamala zaben.

Jam’iyoyi sun nuna rashin amincewa da umurnin, da cewa bai dace hukumar ta hana su yawon rali ba tun da hukumar ta iya daga ranar zabe.

Mun ruwaito da cewa Adams Oshiomhole, ciyaman na Jam’iyyar APC yayi barazanar cewa zasu kaurace wa hukumar INEC akan wannan. “Zamu ci gaba da yakin neman zabe har sai ga zabe” inji shi.

Bayan tattaunawa matakin da hukumar ta yi a ranar Litinin 18, ga watan Fabrairu, 2019, sun amince da sake bada dama ga Jam’iyoyi don fitar yawon rali ga neman zabe har zuwa ranar Alhamis na makon nan.

Hukumar na bada tabbaci da cewa ba za su sake daga ranar zabe ba, kuma zasu magance duk wata matsala cikin makon nan da ake ciki.

Karanta wannan: ‘Yan Hari da makami sun kashe Boniface, Ciyaman na Jam’iyyar APC na Jihar Benue

Advertisement
close button