Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 19 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 19 ga Watan Fabrairun, 2019

1. Shugaba Buhari ya ce ba ya jin tsoron faduwa ga zaben 2019

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari fada da cewa, ba ya jin tsoron rasa cin zaben shugaban kasa da aka daga ranar Asabar da ta gabata zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa shugaba Buhari ya yi wannan furdan ne a wata zaman ganawa ta manyan ‘yan Jam’iyyar APC da suka yi ranar Litinin a hedkwatar na jam’iyyar da ke a birnin Abuja game da jinkirta zaben.

2. INEC: Mako daya bai isa ga sake shirin zaben kasa ba – inji Gbenga Olawepo

A yayin da hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ke shirin ganin cewa zaben 2019 ya kasance da kyau, da kuma tabbatar da cewa zaben ya kasanace da rashin makirci hade da samar da tsaro mafi kyau don kare rayuka da kuma magance shirin ta’addanci ga zaben, dan takaran Jam’iyyar (People Trust), Mista Gbenga Olawepo-Hashim, ya bukaci shugaban hukumar INEC da kara binbini da sake gabatar da ranaku mai yawa don magance duk wata matsala kamin ranar zaben ya iso.

“Mako guda da aka sanar don magance matsaloli akan zaben bai isa ba” inji shi Mista Gbenga.

3. Oshiomhole ya zargi hukumar INEC da sanarwa Jam’iyyar PDP da zancen daga ranar zabe

Akwai sani da cewa hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta daga zaben shugaban kasa da ya kamata an fara yi tun ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, 2019 da ta gabata zuwa ranar 23 ga Watan Fabrairu.

Adams Oshiomhole, Ciyaman na Jam’iyyar APC ta tarayya, ya yi zargin cewa hukumar ta sanar wa Jam’iyyar PDP shirin daga ranar zaben kamin kowa ya sani.

Adams ya fadi wannan ne a wata ganawa da Jam’iyyar ta yi a birnin Abuja ranar Litini da ta gabata.

4. Ka kwace akwatin zabe, ka kuma biya da ranka – inji shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a zaman ganawa da yayi da manyan Jam’iyyar APC a hedkwatan su da ke Jihar Abuja, ya bada umarni ga jami’an tsaro da su ci mutuncin duk wanda yayi kokarin kwace akwatin zabe ga zaben shugaban kasa da aka daga zuwa ranar Asabar ta gaba, 23 ga watan Fabrairu, 2019.

shugaban ya bayyana hakan ne a Birnin Abuja lokacin da yake gabatarwa akan zancen zaben bana.

5. Kungiyar IPMAN ta rage tsadar kudin Man fetur don zaben 2019

Kungiyar ‘yan kasuwancin man fetur ta gabatar da rage tsadar kudin man fetur don zaben shekara ta 2019 da ake batun fara wa.

Kungiyar ta bukaci mambobin ta da rage tsadar kudin man daga naira 145 zuwa naira #40.

6. INEC: Za mu ci gaba da hidimar yakin neman zabe – inji APC, da Jam’iyyar PDP

Jam’iyyun siyasa da ke cikin tseren takaran shugabanci ga zaben 2019 sun kaurace wa zance da hukumar INEC ta yi na cewar kada kowa ya kara fita don yakin neman zabe har zuwa rannar da za a fara zaben.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa shugaban hukumar INEC a ranar Asabar da ta gabata, ya dakar da zaben shugaban kasa, kuma ya hana kowa da kara fita don yakin neman zabe.

7. HISBAH na shirin Aurar da Mata 8,000 a ranar guda, a Jihar Kano

Kungiyar Islam da aka fi sani da suna, HISBAH ta gabatar da Zawarawan Mata, Gwamraye da ‘Yan Mata 8,000 da zasu yi daura wa aure a ranar daya.

A bayanin Alhaji Adamu, “gwamnatin Jihar, a jagorancin Gwamna, Abdullahi Ganduje, ta tsarafa wannan shiri ne don dakatar da halin karuwanci a Jihar”.

8. Zan bada tallafin Mota ga duk mai bukatar zuwa gida don zabe – Reno Omokri

Wani sananen dan Najeriya da ke da suna Reno Omokri, wanda ke da wata shirin gidan talabijin na bayanin kirista ya aika a yau Litinin, 18 ga Watan Fabrairu a yanar gizon nishadarwa ta twitter da cewa, ya gane da cewa mutane da yawa basu ji dadin matakin da hukumar zaben kasa, INEC ta dauka ba, na daga ranar zaben shugaban kasa.

“Duk mai muradin tafiya ya bincika layin twitter di na @renoomokri ranar Laraba don samun cikakken bayani akan yada za a halarci wajen shigan mota”

“Zan bada tallafin motoci don matafiya da ke bukatar zuwa gida don jefa kuri’a su

Ka sami cikakkun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa