Connect with us

Labaran Najeriya

Sai Buhari, Sai NextLevel – Aisha Buhari ta gabatar goyon bayan ta ga mijinta

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Matan shugaban kasar Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari ta gabatar da goyon bayan ta game da bayanin shugaba Muhammadu Buhari akan lamarin zaben shugaban kasa da za a yi ranar Asabar ta makonnan.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa shugaba Buhari yayi wata furci a yayin da yake gabatarwa a zaman da suka yi ranar Litinin a hedkwatar jam’iyyar.

Inda shugaban ya fada da cewa, “duk wanda ya kwace, ko sace akwatin zabe, yayi haka ne don rasa rayuwarsa”

Shugaban ya kara da cewa, duk da cewa hukumar INEC ta daga zaben zuwa Asabar mai zuwa, baya jin tsoron haka don yana da tabbacin cewa zai lashe zaben.

“Duk wanda yayi kokarin sace akwatin zabe, yayi hakan ne don munsayar ransa” inji Buhari.

Aisha Buhari da ganin wannan, sai ta aika a shafin yanar gizon nishadi ta twitter da take amfani da shi, ta ce “Buhari ke nan da shirin kai Najeriya zuwa (NextLevel) gaba.

Sakon na kamar haka;

👍👍👍👍👍👍👍 #ThisIsGMB taking Nigeria to the #NextLevel