Connect with us

Labaran Najeriya

Zaben 2019: Zan bawa Buhari kuri’un mutane Miliyan 2 – inji Abacha

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takaran Gwamnan Jihar Kano, Mohammed Abacha, daga Jam’iyyar APDA (Advance Peoples Democratic Alliance)  ya gabatar da goyon bayan shi ga shugaba Muhammadu Buhari ga zaben shugaban kasa da za a yi ranar Asabar ta gaba.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Mohammed Abacha ya kasance da na farko ne ga marigayi, tsohon shugaban kasan Najeriya Janar Sani Abacha.

“Zan taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari da kuri’un mutane kimanin Miliyan 2 daga Jihar Kano don ganin cewa ya samu lashe zaben shugaban kasa ta shekarar 2019” inji Abacha, a wata bayanin shi da manema labarai a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu da ta gabata a Jihar Kano.

Da aka tambaye shi dalilin da yasa ya mara wa shugaba Muhammadu Buhari ba tare da sanin ciyaman na Jam’iyyar APDA, Bashir Bataya ba, sai ya ce “na gabatar da hakan ne ganin irin ci gaba da ayuka da shugaba Buhari yayi tun lokacin da ya hau mulki a shekarar 2015”

“Buhari ya samar da tsaro, ribato tattalin arzikin kasar, da kuma samar da manyan ayukan da ya taimaka wajen aikin noma” inji shi.

Ya kuma samar da ayuka da dama ga Matasa, hade da hidimar bayar da abinci ga ‘yan makarantar sakandari da firamare.

Mun ruwaito a baya da cewa kungiyar mallaman makarantar sakandare sun bukaci gwamnatin tarayya da dakatar da shirin dafa abinci ga ‘yan makarantan sakandari da firamare da gwamnatin ke yi.

“Zai fi kyau a yi amfani da kudaden nan wajen sake tsarafa da kuma gyara makarantu da suka lallace a jihohi, ko kuma sayan kayakin fasaha da zai amfani kowane yaro” inji NUT a wata ganawa da suka yi.