Bidiyo: Rundunar Sojojin Sama sun rusa Bam ga wajen kwancin 'yan Boko Haram | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labarai Hausa

Bidiyo: Rundunar Sojojin Sama sun rusa Bam ga wajen kwancin ‘yan Boko Haram

Published

Rundunar Sojojin saman Operation Lafiya Dole ta Najeriya sun watsa bam a wajen zaman ‘yan ta’addan Boko Haram da ke a Jihar Borno.

Sojojin sun bayyana a wata Bidiyo yadda suka watsa bam a wajen kwancin ‘yan Boko Haram da ke a yankin Arboko, a nan Jihar Borno, sun kuma samu ribato wasu makaman yakin a wajen.

Sun kai wa ‘yan ta’addan hari ne daga sama a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2019.

Mun samu tabbacin wannan ci gaba ne a Naija News ranar Laraba 20 ga watan Fabrairu daga bakin wani kwamandan Sojojin, Air Commodore Ibikunle Daramola, Daraktan yada labarai ga rundunar sojojin sama ta Najeriya.

Ya bayyana da cewa rundunar sojojin na iya kokarin su da ganin cewa sun sha karfin ‘yan ta’addan har ga cin nasarawa.

Kalli bidiyon;

 
Kuna iya aika Naija News ta hanyar amfani da maɓallin rabar mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa [email protected].