Connect with us

Uncategorized

Dan takaran Sanata a Jihar Kwara ya kure mutuwa sakamakon harbin ‘yan hari da bindiga

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan hari da bindiga sun fada wa dan takaran sanata na Jam’iyyar APC na Kudu ta Jihar Kwara, Hon. Lola Ashiru.

Ko da shike Ashiru ya samu tsira daga harin, amma dai rahoto ta bayar da cewa ‘yan harin sun samu kashe wasu daga cikin mabiya bayan sa wajen yawon yakin neman zabe a Jihar.

Wannan harin ya faru ne ranar Talata 19, ga watan Fabrairu da ta gabata a garin Oyun dadare.

Bincike ta bayar da cewa wasu daga cikin mabiyan na Ashiru sun tsira da raunuka sakamakon harin.

Mun ruwaito a baya da cewa Sanata da ke wakiltar Jihar Kogi ta tsaka, Sanata Ahmed Ogembe ya tsira daga wata mugun hadarin mota a hanyar da ta bi Abuja zuwa Lokoja, a yayin da yake kan hanyar zuwa Okene don hidimar zaben.

 

Karanta wannan kuma: Zan bada tallafin Mota ga duk mai bukatar tafiya zuwa gida don zabe ranar Asabar  – Reno Omokri