Connect with us

Uncategorized

Kungiyar ‘Yan Shi’a sun kara fita zanga-zanga bukatar a sake El-Zakzaky

 

A yau Laraba, 20 ga watan Fabrairu, 2019, Kungiyar ‘yan shi’a sun sake kafa kai ga zanga-zanga a gaban Ofishin Harkokin Waje da ke a birnin Abuja da ikirarin cewa a sake shugaban su.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa gwamnatin tarayya a shugabanci shugaba Muhammadu Buhari sun kame shugaban ‘yan shi’a, El-Zakzaky da matarsa Zeenat tun watan Disamba ta shekarar 2015.

Rahoto ta bayar da cewa ‘yan kungiyar sun yi amfani da damar nan ne don jawo hankalin masu hangen nesa ga zaben 2019 da suka shigo kasar Najeriya daga kasashen waje don kula da hidimar zaben 2019. “wata kila ko yin hakan zai taimaka wajen sake shugaban su” inji rahotanni.

Muna kuma da sani a Naija News da cewa gwamnatin tarayya taki sake shugaban ne da matarsa akan wata dalili da ba mu san da ita ba, duk da cewa kotu ta bayar da umurni da cewa an saki El-Zakzaky da matarsa.

Mun tuna da sanar a baya da cewa kungiyar sun yi barazanar cewa ba zasu raunana ba, kuma ba zasu ja da baya ba sai har sun samu kubutar da shugaban su

Advertisement
close button