Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 20 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 20 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Dalilin da ya sa ban amince da Buhari game da zance kashe wandada ke shirin sace akwatin zabe – Farfesa Mahmood (INEC)

Shugaba hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya mayar da martani game da furcin shugaba Muhammadu Buhari akan masu sace akwatin zabe.

Ya ce, “A dubi na, ya kamata ne a yi hukunci ga irin wadannan mutane kamar yadda take a cikin dokar zaben kasa, amma ba kashe su ba kamar yadda shugaban ya furta”.

2. Leah Sharibu ta kai shekara daya a kangin Bokon Haram

A ranar jiya Talata, 19 ga watan Fabrairun, daya daga cikin ‘yan makarantan Dapchi da ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace kwanakin baya, Leah Sharibu ta kai shekara daya a hannun ‘yan ta’addan.

“Ina ganin Leah a mafarki na kulluma, ta kan zo mani da kira na ‘Baba kuna lafiya ko?” inji tsohon yarinyar, Mista Nathaniel Sharibu, kamar yadda ya bayyana ga manema labarai.

3. Tsohon shugaban Sanatocin Najeriya na zargin Obasanjo da Jam’iyyar PDP da shirin raunan kasar Najeriya

A yayin da ake shirin zaben ranar Asabar ta makon nan, tsohon shugaban sanatocin Najeriya, Ameh Ebute ya zargi tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo tare da Jam’iyyar PDP cewa suna kokarin raunana kasar Najeriya.

“Hadin kai da ke tsakanin Obasanjo da Jam’iyyar PDP, shiri ce na kadamar da makirci da kuma jawo kashe-kashen rai a kasar” inji Mista Ebute.

4. Ba za a lallace dimokradiyyar kasar Najeriya ba saboda gurin mutun guda  – Sanata Saraki

A wata zama da Jam’iyyar PDP suka yi na tattaunawa game da lamarin zaben 2019, a hedkwatan Jam’iyyar da ke a birnin Abuja a ranar 19 ga watan Fabrairu, 2019. Sanata Bukola saraki ya furta da cewa “Ba za a lallace dimokradiyyan kasar Najeriya ba saboda gurin mutun guda kawai” inji shi.

Wannan itace bayanin Sanata Bukola Saraki, shugaban jagorancin lamarin zabe ga dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

5. Ya kamata Buhari yayi kirar ganawa da Majalisar Jihohin kasa –  inji Gwmana Dickson

Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson ya fada da cewa, ya kamata shugaba Muhammadu Buhari ya gana da majalisar jihohin kasa don tattaunawa akan zaben 2019.

Dickson ya gabatar da wannan ne a yayin da yake bayani da manema labarai a birnin Yenagoa, babban birni Jihar Bayelsa.

Ya ce “Ya kamata shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawa ta musanman da Majalisar Jihohi don tattaunawa akan daga ranar zaben kasa da hukumar INEC ta yi, da kuma tattaunawa akan yadda za a kadamar da zaben ranar Asabar ba tare da wata matsala ba.

6. Atiku yayi karar naira Biliyan N2b ga shugaba Muhammadu Buhari

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kalubalanci Kotun kara ta birnin tarayya da cewa su umurci shugaba Muhammadu Buhari hade da hukumomin tsaro da janye hannun su ga hidimar zaben 2019.

Dan takaran ya kara da bukatar kotun da cin karar shugaba Buhari akan zargin karya da aka yi masa a baya, da kuma wallafa wasikar roko ta fili gareshi.

7. Kashe-kashe ya haura a Jihar Kaduna – Nasir El-Rufai

Gwamnar Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana da cewa ana kokarin watsar da wasu yankuna da ke a Jihar Kaduna.

Wannan itace bayanin El-Rufai a yayin da yake gabatarwa a gidan majalisar jihar, da cewa kashe-kashe a Jihar Kaduna ya haura daga kashi 66 zuwa kashi 130.

8. Shugaba Muhammadu Buhari yayi ganawa da hukumomin tsaro da manyan shugabannan Jihohi

A jiya Talata, 19 ga watan Fabrairu, shugaba Muhammadu Buhari yayi wata ganawa ta gaggawa da hukumomin tsaron kasa hade da manyan shugabannan jihohi da Ministoci akan lamarin tsaro ga zaben  2019.

An yi wannan zaman tattaunawar ne a Ofishin shugaban a misalin karfe 11 na safiya a anan birnin tarayya, Abuja.

9. Hukumar EFCC sun kame Lauyan dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar

Hukumar sun kame Mista Uyiekpen Giwa – Osagie ne da maraicen ranar Litini da ta gabata, akan wasu zargi 18 da ake tugumar shi da ita na cin hanci da rashawa.

Wata rukuni ta bayar da cewa wata kila mista Osagie da Jam’iyyar PDP na shirin yin amfani da kudaden ne da ake zargin sa da ita wajen gudanar da makirci da sayen zabe ga zaben shugaban kasa da za a yi a ranar Asabar ta gaba.

Ka sami cikakkun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa