Connect with us

Uncategorized

Sabuwa: Mahara sun kashe mutane 16 a Jihar Benue

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan hari da bindiga sun kai wata sabuwar hari a Jihar Benue

Wasu mahara da bindiga sun yi wata sabuwar hari inda suka kashe kimanin mutane 16 a Jihar Benue. An yi wannan harin ne a ranar Laraba, 20 ga watan Fabrairu a karamar hukumar Agatu da ke a Jihar Benue.

An sanar mana a Naija News ne da cewa maharan sun kai harin ne a yankin misalin karfe 1 na safiyar ranar Laraba da ta gabata, inda suka fada wa gidaje da harbe harben bindiga.

Ko da shike da aka binciki Kwamanda ‘yan tsaron Jihar, Mista Adeyemi Yekini, ya baya da cewa bai da tabbacin kimanin mutane da suka mutu ko samu raunuka a sakamakon harin.

Wani mai suna Daddy Seni ya gabatar wa manema labarai da cewa Baban sa da ‘yan uwar sa na cikin mutanen da maharan suka kashe.

Naija News Hausa ta gane da cewa duk da barazana da jami’an tsaro ke yi game da samar da tsaro a kasar, bai hana ko rage hare-hare ba a wasu jihohin kasar, musanman Jihar Benue.

Yekini ya kara da cewa rundunar sojojin sun sun watsar da sojoji a inda abin ya faru don bincike da kokarin kame wadanda suka aikata wannan.

“Gwamna Samuel Ortom, Gwamnan Jihar Benue na da tabbacin wannan harin kuma ya riga ya gana da kwamishanan ‘yan sandan Jihar, Mista Bishi don daukan mataki akan wannan” inji Iterver Akase, Babban sakataren gwamnan Jihar.

“Wannan abin takaici ne saboda gwamnan ya gane da cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ke gudanar da wannan don jawo tsoro da tashin hankalin mutane ga kulawa da hidimar zaben shekarar 2019″ inji shi.

 

Karanta wannan kuma: Rundunar Sojojin Sama sun rusa Bam ga wajen kwancin ‘yan Boko Haram