Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 21 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 21 ga Watan Fabrairun, 2019
1. Atiku dage da sayar da kamfanin NNPC
Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya dage da cewa zai sayar da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) idan har ya lashe zaben ranar Asabar, 23 ga Watan Fabrairu, 2019.
Dan takaran ya sake kafa baki ne ga wannan batun a yayin da yake wata ganawa da manyan shugabannan kananan hukumomi da Jam’iyya a Jihar Kaduna.
2. Jam’iiyar APC a Jihar Rivers sun bukaci hukumar INEC ta basu daman tseren zabe
Jam’iyyar APC na Jihar Rivers sun wallafa wata wasika zuwa ga hukumar gudanar da zaben kasa (INEC). A cikin wasikar, sun bukaci hukumar ta basu daman shiga tseren takara ga zaben ranar Asabar.
Mun ruwaito a Naija News da cewa hukumar INEC a baya ta dakatar da Jam’iyyar APC a Jihar Rivers don shiga tseren takara ga zaben 2019 akan wasu laifuka da zargi akan ‘yan Jam’iyyar.
3. Kungiyar FEC sun marawa shugaba Buhari baya akan zancen kashe masu shirin sace akwatin zabe
Kungiyar Shugabannan Tarayyar Kasa (FEC) sun bayyana amincewar su game da zancen furci da shugaba Muhammadu Buhari yayi akan cewa “Duk wanda ke shirin sace akwatin zabe ga zaben shekarar 2019 yayi hakan ne a munsayan ransa”.
An gabatar da batun ne daga bakin Ministan Labarai da Al’adun kasa, Lai Mohammed.
4. Gwamnatin Tarayya ta bada umurnin biyan ma’aikata don samun kudin tafiya zuwa zabe
Ganin irin hali da ake ciki na rashin kudi kuma ga zaben kasa ta kusanto, Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin cewa a biya ma’aikata albashin su don samun damar tafiya gida ga zaben ranar Asabar.
Muna da sanin cewa albashin ma’aikata kan shiga asusun ajiyar su ne ranar 25 ga kowane wata, amma wannan karon gwamnatin tarayya ta bukaci a biya su kamin ranar.
5. Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya sun fashe mazaunin Boko Haram a Jihar Borno da Bam
Rundunar Sojojin Sama ta Operation Lafiya Dole sun ci sabuwar nasara akan wata bam ta suka jefa ga kangin Boko Haram da ke a Arboko ta Jihar Borno.
Sun samu cin wannan nasara ne a ranar 18 ga watan Fabrairun, 2019
6. ‘Yar takaran shugaban kasa na Jam’iyyar NIP ya janye daga tseren, ya mara wa Atiku baya
Mallama Eunice Atuejide, da ke takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar NIP ta janye daga tseren takaran, ta kuma bayyana goyon bayan ta ga dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Eunice ta gabatar da wannan ne a ranar Laraba da ta gabata, kwana hudu ga zaben shugaban kasa da zaben gidan majalisa.
7. Hukumar INEC ta karshe zancen zaben Jihar Rivers
Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta kai ga karshen bukatar Jam’iyyar APC a Jihar Rivers ga zaben 2019.
Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu, ya dage da cewa Jam’iyyar ba zasu shiga tseren takaran zaben shekarar ba. kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa a baya da cewa hukumar ta dakatar da Jam’iyyar APC a Jihar Rivers ne akan wata zargi.
8. Shugaba Buhari ya rantsar da Sakatarori 8 na Tarayya
A ranar Laraba da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari, ya rantsar da sabbin sakatarorin tarayya 8 da aka sanya a nan birnin tarayya, Abuka.
Shugaban ya kuma gabatar da su kamin zaman ganawa da yayi da Manyan shugabannan Tarayya.
9. Hukumar INEC ta bayyana ranar da za su gabatar da sakamakon zabe
Hukumar sun bayyana lokacin da za su sanar da sakamakon zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.
“Ba zai dade ba kamar yadda aka gabatar a zaben shekara ta 2015, duk da cewa ‘yan takaran kujerar shugaban kasa sun kara yawa fiye da shekarun baya, zamu sanar da sakamakon cikin lokaci” inji hukumar.
Ka samu cikakun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa