Connect with us

Uncategorized

Yadda Cutar Lassa Fever ta kashe mutane 10 a Jihar Plateau

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mugun cuta da ya kashe mutane da dama a kasar Najeriya shekarun baya ya sake kashe mutane goma (10) a Jihar Filatu.

Mun samu rahoto a Naija News Hausa da cewa cutar ya kashe mutane goma ne kuma an iya gane da cewa kimanin mutane 28 aka gane da ke kame da cutar a Jihar.

Kwamishanan kulawa da lafiyar jiki na Jihar, Dakta Kunden Deyin, a bayanin sa da manema labarai ya bayyana da cewa mutane 64 aka kai asibiti don bincike da kamuwar ciwon. “bayan binciken, an iya gane da cewa mutane 28 ke kame da ciwon a halin yanzu daga cikin mutane da aka kai bincike, sa’anan kuma mutane goma suka mutu daga cikin su” inji shi.

Ya gabatar da wannan ne a yau, Alhamis, 21 ga watan Fabrairu, 2019. Ya ce, wadanda ke kame da ciwon sun tsiro ne daga Jihar Kaduna, amma a halin yanzu suna asibiti don isashen kulawa.

Daktan ya shawarci mutane da cewa su sanar da duk wata alamun kamuwa da cutar. “Cutar Lassa Fever na kamar cutar zazzabi ne, duk wanda ya gano wani ko wata da alamun, ko kuma da ke kamuwa da wannan ya yunkura zuwa asibiti don cikakken bincike” Dakta Deyin.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa cutar Lassa Fever ya dauke rayuka 5 a Jihar Plateau

Dakta Deyin ya kara shawartan mutane da cewa su dinga nuna kulawa ta gaske a wajajen zaman su, da kuma tabbatar da cewa beraye basu mamaye su ba don rage yaduwar cutar.

 

Karanta wannan kuma: HISBAH na shirin Aurar da Mata 8,000 a ranar guda, a Jihar Kano