Connect with us

Uncategorized

Kotun Jihar Legas ta bukaci kame tsohon dan kwallon Najeriya, Jay Jay Okocha

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kotun koli ta Igbosere, a Jihar Legas ta bada umarnin kame shahararen dan wasan kwallon kafa ta Najeriya, Jay Jay Okocha.

Kotun ta bukaci kame Austin Okocha, da aka fi sani da suna ‘Jay-Jay Okocha akan zargin cewa dan tsohon dan kwallon Najeriya da Kaftin din ‘yan wasan ya ki biyar kudin harajin sa da tsawon kwanaki.

Mun samu tabbaci da cewa kotun a ranar 6 ga watan Yuni a shekarar 2017 sun bukaci dan kwallon da ganawa da kotun akan zargin da ake da shi na rashin biyar kudin harajin sa, amma Okocha yaki biyaya ko nuna kulawa da hakan.
mun kuma gane a Naija News da cewa kotun ta sake kiran Okocha a ranar 5 ga watan Aktoba, 2017 amma yaki halarta ko nuna kulawa da haka.

Bayan da kotun suka gane da cewa Okocha yaki biyaya da kira da aka yi masa na bukatar sa da halartan kotu don neman bayanin akan dalilin da ya sa yaki biyan harajin sa, sai kotun ta dauki matakin bada umarni da kame shi.

Alkalin da ke karar, Mista Adedayo Akintoye, a ranar 29 ga watan Junairu ya bada umarni cewa a kame Okocha don rashin biyar harajin sa da rashin amsa kira da kotun ke ma sa tun shekarun baya.

An bayyana da cewa ya kamata ayi hukunci ne akan dan wasan kwallon a watan Fabrairu amma kotun ta daga karar zuwa ranar 15 ga watan Afrilu, a shekara ta 2019 don kamala karar Okocha.

“Kotun ta bayyana da cewa Okocha ya karya dokar kasan ne na rashin biyar harajin sa yadda ta ke ga dokar kasa, kamar yadda aka sake tsarafa ta a tun shekarar 2004” inji Alkali Adedayo.

Karanta wannan kuma: Bincike ya bayyana yadda Cutar Lassa Fever ta kashe mutane 10 a Jihar Plateau