Connect with us

Uncategorized

PDP sun yi ta’aziyya ga mutane 130 da suka mutu a Jihar Kaduna

 

Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna a ranar Alhamis da ta gabata sun yi gaisuwar jinya ga gwamnatin Jihar Kaduna da iyalan mutane 130 da suka mutu sakamakon wata hari da mahara da bindiga suka kai a karamar hukumar Kajuru a Jihar.

Jam’iyyar sun gabatar da gaisuwar ne daga bakin Mista Felix Hyat, Ciyaman na Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, a wata zaman tattaunawa da aka gudanar a Jihar.

A bayanin Mista Hyat, ya kalubalanci hukumomin tsaro da bayani akan yadda ‘yan ta’adda suka samu kashe kimanin mutane 130 a cikin mako daya a Jihar.

“Dole ne hukumomin tsaron Jihar su bamu bayani ta musanman yadda aka kashe rayuka 130 a cikin mako daya a Jihar” inji shi.

“Abin takaici ne gane irin yadda rayuka ke ta mutuwa a Jiha Kaduna ba tare da an magance hakan ba. Rayukar mutane ya zama kamar wata abin banza da za a ta kashewa a kowane lokaci”

“Muna gabatar da ta’aziyar mu ga iyalan wadanda abin ya sama, Allah ya jikan rai” inji Hyat.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa ‘yan hari da bindiga sun sace mutane 16 a Jihar Benue a ranar Alhamis da ta gabata

“A koyaushe cikin makonnai da suka wuce, ana sanar wa a gidan yada labarai da mumunar sanarwa akan yadda mutane ke mutuwa a Jihar Kaduna sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda da rukunin ta’addanci ‘yan siyasa” inji shi.

Haka kuma gwamnar Jihar, Malam Nasiru El-Rufai, a ranar 15 ga watan Fabrairun ya gabatar da mutuwar mutane 66 a karamar hukumar Kajuru, sakamakon wata hari da aka kai wa Fukanin Jihar.
“An gabatar da irin wannan mumunar harin ne ‘yan awowi kadan da soma zaben shugaban kasa a ranar 16 ga watan Fabarairu, Asabar da ta gabata, kammar yada aka shirya zaben kasar a baya kamin aka daga zaben zuwa ranar 23”

“Wannan abin takaici ne. Amma tun da gwamna El-Rufai ya bada tabbacin tsaro ga zaben shugaban kasa da ta gidan Majalisa ta ranar Asabar, mu ma daga jam’iyyar PDP, muna goyon bayan hakan. Zamu kuma tabbatar da cewa mun magance duk wata matakin tashin hankali ga zaben 2019” inji Hyat.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya aika wakilai don isar da sakon ta’aziyya ga Iyalan mutane 8 da suka mutu wajen Rali a Jihar Taraba – Buhari

Advertisement
close button